Hukumar EFCC Ta Gabatar da Jami'in Binance a Gaban Kotu, Bayanai Sun Fito

Hukumar EFCC Ta Gabatar da Jami'in Binance a Gaban Kotu, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gabatar da jam'in kamfanin Binance a gaban kotu
  • Jami'an hukumar ne dai suka gabatar da Tigran Gambaryan a gaban kotu domin fara shari'a kan tuhume-tuhumen da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin
  • Ana dai zargin kamfanin da ƙin biyan hukumomi kuɗaɗen haraji duk da ɗumbin hada-hadar maƙudan kuɗaɗe da ƴan Najeriya ke yi a ƙarƙashinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami'in kamfanin 'Binance Holdings Limited', Tigran Gambaryan, ya bayyana a gaban kotu bisa zargin ƙin biyan haraji.

A yau ne ake sa ran gurfanar da shi tare da Nadeem Anjarwalla wanda ya arce a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa gwamnatin Tinubu ta shirya ninka kudin wutar lantarki

EFCC ta gurfanar da jami'an Binance gaban kotu
Ana zargin Binancen da kin biyan haraji Hoto: @OfficialEFCC, @Naija_PR
Asali: Twitter

Wace tuhuma ake yi wa Binance?

A cikin ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CR/115/2024, an zargi Binance da gaza yin rajista tare da hukumar tattara haraji ta tarayya, saboda ayyukan da suke gudanarwa a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar FIRS ta yi zargin cewa kamfanin ba ya bada shaidar abubuwan da yake yi ga mutanen da ke hada-hada da shi ta yadda za a iya gane adadin harajin da ya kamata ya biya.

Jaridar TheCable ta ce jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ne suka kawo Gambaryan zuwa cikin kotun.

A yayin zaman kotun, an ɗage sauraron shari'ar har sai zuwa ranar, 19 ga watan Afirilun 2024, saboda gazawar hukumar FIRS wajen sanar da Gambaryan laifuffukan da ake tuhumarsa, yayin da yake tsare a hannun EFCC.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanya mutane farin ciki awanni 24 bayan sace kananan yara 30 a Arewa

Gambaryan ya shigar da ƙara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'in kamfanin Binance da ke tsare a Najeriya ya maka mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da hukumar EFCC a gaban kotu.

Tigran Gambaryan ya shigar da ƙarar ne bisa abin da ya kira tauye masa haƙƙinsa da aka yi kan ci gaba da tsare shi da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel