'Yan Bindiga Sun Sanya Mutane Farin Ciki Awanni 24 Bayan Sace Ƙananan Yara 30 a Arewa

'Yan Bindiga Sun Sanya Mutane Farin Ciki Awanni 24 Bayan Sace Ƙananan Yara 30 a Arewa

  • Ƙananan yara 30 da ƴan bindiga suka sace a kauyen Kasai da ke yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun shaƙi iskar ƴanci
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya ce masu ruwa da tsaki a yankin sun taimaka wajen ceto yaran
  • Ya ce dakarun ƴan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin sace yaran domin kama dukkan masu hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - A wani lamari mai ban mamaki, kananan yara 30 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Kasai da ke ƙaramar hukumar Batsari a Katsina sun kuɓuta.

Yaran sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya ƙasa da sa'o'i 24 bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da su, jaridar Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, mutane da yawa sun mutu

IGP Kayode.
Yan bindigan sun sako kananan yara a Katsina Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa an yi garkuwa da yaran ne yayin da suka fita bayan gari domin su ɗebo wa iyayensu itacen girki ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma ƙasa da sa’o’i 24, yaran suka shaƙi iskar ‘yanci sakamakon namijin ƙoƙarin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki na yanki.

Yadda aka ceto kananan yaran

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da cewa yaran sun kuɓuta a ranar Talata.

"Biyo bayan kokarin da rundunar ƴan sanda ta yi kan lamarin tare da taimakon masu ruwa da tsaki, mun yi nasarar cimma sakamako mai kyau," in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa an samu nasarar ceto yaran ne sakamakon matakin gaggagwa da hukumomi suka ɗauka bayan samun rahoton abin da ya faru.

Kakakin ƴan sandan ya kuma tabbatar wa da al'umma cewa dakarun ‘yan sanda sun maida hankali wajen gudanar da bincike sosai kan lamarin domin kamo masu hannu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin rashin imani ana azumi, sun yi garkuwa da kananan yara 30 a Arewa

Mutanen kauyen sun yi farin ciki

Muhammad Batsari, mazaunin yankin da lamarin ya auku a Katsina, ya tabbatar da labarin sakin yaran, Channels tv ta ruwaito.

Cikin tsananin farin ciki da faruwar lamarin, Batsari ya ce, “Na samu kiran waya da safiyar yau, inda aka sanar da ni cewa ‘yan bindigar sun sako dukkan wadanda suka sace."

Ƴan bindiga sun kai hari a Gusau

A wani rahoton kuma 'yan bindiga sun shiga har cikin gidan wani ɗan kasuwa, sun kashe shi tare da sace matarsa da maƙwabcinsa a jihar Zamfara.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Shehu Muhammad Dalijan, ya tabbatar da faruwar lamarin a Gusau, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel