Tunji-Ojo: Badakalar Betta Edu da Wasu Zarge-Zarge 2 da Ake Yi Wa Ministan Tinubu

Tunji-Ojo: Badakalar Betta Edu da Wasu Zarge-Zarge 2 da Ake Yi Wa Ministan Tinubu

  • Akwai wasu manyan badakaloli da ake zargin akwai sa hannun ministan Tinubu, Mr. Olubunmi Tunji-Ola a ciki, kamar badakalar Betta Edu
  • Yayin da ake ganin ministan harkokin cikin gida ya zama tauraro saboda nasarorin da ya cimmawa, sai dai wadannan badakaloli na binsa
  • Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla kan wadannan badakaloli, tare da kuma bayyana matsayar ministan tarayyar a kan kowacce badakala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ana dai kallon ministan harkokin cikin gida na shugaba Bola Tinubu, Olubunmi Tunji-Ojo a matsayin tauraro a wannan sabuwar gwamnati, saboda dimbin nasarorin da ya samu a cikin watanni shida na farko a kan karagar mulki.

Wasu daga cikin nasarorin sun hada da kammala tarin fasfo na mutane da kuma aiwatar da sabon tsarin sabunta fasfo ba tare da mutum ya je ofishin ma'aikatar ba.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi ya haifawa majalisar dattawa fushin kungiyoyin Arewa

Jerin wasu badakaloli 3 da ake zargin ministan Tinubu ya aikata
Ya zuwa yanzu dai an tuhimi Tunji-Ojo da aikata laifuka uku, wadanda kusan ya musanta su.Hoto: Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Twitter

Sai dai ministan yana da manyan badakaloli guda uku a tarihinsa wanda yawancin ‘yan Najeriya ke da masaniya a kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin badakalolin a kasa:

1. Badakalar Betta Edu

A kwanakin baya ne aka tuhumi ministar harkokin cikin gida da karbar kwangilar Naira miliyan 438.1 daga hannun tsohuwar ministar jin kai da rage radadin talauci, Betta Edu.

Arise News ta ruwaito cewa an yi zargin Tunji-Ojo ya karbi kwangilar ne ta hanyar wani kamfani New Planet Project Limited, da ake zargin mallakarsa ne.

New Planet Project Limited ya kasance daya daga cikin kamfanoni masu yawa da ake zargin Edu ta basu kwangilar shirin ba da tallafi wanda ta kashewa Naira biliyan 3.

A nasa martanin ministan ya ce ba shi da da hannu a wannan badakala saboda ba ya cikin shugabannin kamfanin a yanzu.

Kara karanta wannan

Gaza: Bam ya kashe ‘yanuwa 36 lokacin shirin sahur a dauki azumin Ramadan

Ga bidiyon martanin da ya yi:

2. Badakalar takardar shaidar NYSC

A rahoto Premium Times, Sanata Sadik Umar ya nuna damuwa kan rashin ingancin takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) ta Tunji-Ojo.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a yayin tantance Tunji-Ojo na zama minista, ya tambayi dalilin da ya sa wanda aka nada ya fara bautar kasa da shekaru 37, amma takardar ta NYSC ta nuna wani kwanan wata na daban.

Sai dai Tunji-Ojo ya yi watsi da batun dan majalisar, inda ya bayyana cewa mutum na iya yin bautar kasa a kowane lokaci bayan kammala karatunsu muddin sun kammala kafin su kai shekaru 30.

A takardar shaidar NYSC, Tunji-Ojo ya yi ikirarin cewa ya shiga aikin yi wa kasa hidima tsakanin watan Nuwamba 2019 zuwa Nuwamba 2020.

Sai dai sanatan ya nuna mamaki na yadda wanda aka nada ya yi NYSC din sa a daidai lokacin da ya ke kan kujerar dan majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC zai rage farashin kayan abinci da 25% yayin da aka fara azumi

Ga takarar kammala NYSC din Tunji-Ojo a kasa:

Takardar kammala bautar kasa ta Olubunmi Tunji-Ojo
Ana zargin akwai rashin gaskiya a takarar kammala bautar kasa ta Olubunmi Tunji-Ojo. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

3. Akpabio da majalisa: "A kashe abin magana"

Kafin a nada shi minista, Tunji-Ojo dan majalisar wakilai ne, mai wakiltar mazabar Akoko a Ondo.

‘Yan Najeriya da dama ba su san cewa ministan harkokin cikin gida shi ne tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) ba.

Channels TV ta ruwaito Godswill Akpabio tsohon ministan harkokin Neja Delta na lokacin, ya bayyana a gaban kwamitin bisa zargin karkatar da kudade na hukumar.

A yayin da ya ke kare kansa a gaban kwamitin, wanda ake yadawa a gidan talabijin kai tsaye, shugaban majalisar dattijai na yanzu ya zargi Tunji-Ojo da sauran ‘yan majalisar dokokin kasar da karbar kwangiloli daga hukumar NDDC.

Sai dai, Tunji-Ojo dai ya musanta zargin inda ya kalubalanci Akpabio da ya kawo shaida.

Ga bidiyon hirar a kasa:

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Tinubu na shirin korar ministoci

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa akwai wani shiri da shugaban kasa Bola Tinubu ya ke yi na sallamar wasu daga cikin ministocin gwamnatinsa.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasar Najeriya ne suka bayyana hakan inda suka ce Tinubu ya sha alwashin korar duk wani minista da ba ya aikin azo a gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel