NEC: Gwamnoni 16 Sun Goyi Bayan Kirkiro Ƴan Sandan Jihohi Domin Dawo da Zaman Lafiya

NEC: Gwamnoni 16 Sun Goyi Bayan Kirkiro Ƴan Sandan Jihohi Domin Dawo da Zaman Lafiya

  • Aƙalla gwamnoni 16 ne suka ayyana goyon bayan kafa rundunar ƴan sandan jihohi yayin da matsalar tsaro ke kara karuwa a Najeriya
  • Majalisar tattalin arzikin ƙasa ta tabbatar da haka ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 21 ga watan Maris bayan kammala taro
  • Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya yi ƙarin haske kan ragowar gwamnoni 20 da birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Biyo bayan taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya, gwamnoni 16 sun goyi bayan kirƙiro ƴan sandan jihohi a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024.

Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) ce ta bayyana haka a rahoton da ta miƙa wa majalisar a wurin taron karo na 140 wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Shugaba Tinubu tare da gwamnoni.
Gwamnoni 16 cikin 36 suna son a kafa yan sandan jihohi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Taron wanda ya gudana ta hanyar amfanin da fasahar zamani ya kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene matsayar sauran gwamnoni?

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa, Alhaji Atiku Bagudu, wanda ya zanta da ƴan jarida ta intanet bayan kammala taron, ya ce sauran jihohin ba su faɗi matsayarsu ba.

Bagudu ya bayyana cewa jihohi 20 da babban birnin tarayya Abuja ba su sanar da matsayarsu kan batun kafa ƴan sandan jihohin ba har kawo yanzu.

Sai dai Bagudu, tsohon gwamnan jihar Kebbi bai ambaci sunayen jihohin da suka goyi baya da waɗanda suka yi shiru kan lamarin ba.

Ya ƙara da cewa gwamnonin da suka mika takardar goyon bayan kirkiro ƴan sandan, sun kuma nemi a sake garambawul ga kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Kotu ta yi hukunci kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB

Gwamnati ta fallasa masu ɗaukar nauyun ta'addanci

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan kwamitin sanya takunkumi ya faɗi sunayen mutane 9 da kamfanonin ƴan canji 6 da ake zargin suna ɗaukar nauyin ta'addanci.

A halin yanzu dukkan waɗanda ake zargin suna ƙarƙashin takunkumi saboda kallon da ake masu na taimakawa ƴan ta'adda da kuɗaɗe.

A rahoton Daily Trust, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mamban ƙungiyar ta'addanci Ansarul Muslimina Fi Biladissudam ne, wadda ke da alaƙa da Al-Qaeda.

Tinubu ya yi sabon naɗi a gwamnati

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mista Olugbile Holloway a matsayin sabon shugaban hukumar kula da gidajen tarihi ta ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel