Bola Tinubu Ya Kori Mutumin Buhari, Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Kula da Kayan Tarihi

Bola Tinubu Ya Kori Mutumin Buhari, Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Kula da Kayan Tarihi

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mista Olugbile Holloway a matsayin sabon shugaban hukumar kula da gidajen tarihi ta ƙasa
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024
  • Holloway zai maye gurbin Farfesa Abba Tijani, wanda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa a watan Augusta, 2020

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Olugbile Holloway a matsayin darakta janar na hukumar kula da gidajen tarihi da kayan tarihi ta ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

NEC: Gwamnoni 16 sun goyi bayan ƙirkiro ƴan sandan jihohi domin dawo da zaman lafiya

Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu ya yi sabon naɗi a hukumar kula da ababen tarihi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya maye gurbin mutumin Buhari

Mista Holloway ya maye gurbin Farfesa Abba Tijani, wanda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa ranar 26 ga watan Agusta, 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zama cikakken darakta janar/shugaban hukumar kula da gidajen tarihi na takwas a tarihi.

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, Dada Olusegun, ya wallafa sanarwar wannan naɗi a shafinsa na manhajar X.

A cewar sanarwan, Mista Holloway ya karanci ilmin siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a digirinsa na farko yayin da ya karanta harkokin kasuwannci a digiri na biyu.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban ƙasa na fatan sabon darakta janar zai farfaɗo da wannan hukuma mai matukar muhimmanci da kuma tabbatar da tsaro, bunkasa da haɓaka al'adun Nijeriya iri daban-daban na zahiri da waɗanda ba a taɓa gani ba."

Kara karanta wannan

Tinubu ya haramta wa ministoci fita ƙasashen waje, an samu karin bayani

Wannan na zuwa mako ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya naɗa Dakta Temitope Ilori a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cutar kanjamau ta ƙasa (NACA).

CBN ya biyan bashin $7bn?

A wani rahoton na daban Saɓanin ikirarin CBN, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje sun musanta cewa an biya su kuɗaɗensu da suka maƙale

Babban bankin Najeriya (CBN), a wata sanarwa, ya bayyana cewa ya biya waɗannan kuɗaɗe na kamfanonin da suka makale a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel