Tinubu Ya Haramta Wa Ministoci Fita Ƙasashen Waje, an Samu Karin Bayani

Tinubu Ya Haramta Wa Ministoci Fita Ƙasashen Waje, an Samu Karin Bayani

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya haramta wa ministoci da sauran muƙarraban gwamnati tafiye-tafiye zuwa waje
  • A cewar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, matakin zai rage kashe kudin jama'a
  • Sai dai Gbajabiamila ya ce ministan ko muƙarrabi na iya neman amincewar Tinubu idan tafiyar ta zama dole

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya haramta wa ministoci, shugabannin hukumomi da sauran muƙarraban gwamnati fita ƙasashen waje.

Bola Tinubu ya yi magana da ministoci da mukarraban gwamnati
Tinubu zai rage kashe kudaden jama'a ta hanyar haramta wa mukarraban gwamnati fita waje. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wannan dokar za ta yi aiki na tsawon watanni uku daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 1 ga watan Yuli.

Matakan rage yawan tawagar Tinubu

Kara karanta wannan

Hukuncin da za a yanke wa iyayen da yaransu ba sa zuwa makaranta a Najeriya

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila wanda ya fitar a ranar 12 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Janairu, Tinubu ya bayar da umarnin rage yawan muƙarraban da ke yi masa rakiya zuwa tafiye-tafiye na gida da waje.

A lokacin ya ce tawagarsa ba za ta riƙa wuce mutane 25 a tafiye-tafiye na gida ba, ko mutum 20 a tafiyar waje.

An soki yawan tura mukarrabai waje

Ya kuma ba da umarnin cewa jami'an tsaron garin da zai kai wa ziyara ne za su ba shi tsaro maimakon ya debi jami'ai da yawa daga Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan sukar da ya sha biyo bayan taron COP28 da aka gudanar a UAE, inda wakilan Najeriya 590 suka halarci taron.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nuna damuwa kan abin da 'yan majalisu ke yi wa ministocinsa, ya kawo mafita

Sai dai a lokacin gwamnati ta yi martani na cewa wakilai 422 ne kawai ta dauki nauyinsu a tafiyar, sauran sun je ne a ƙashin kansu.

Tinubu zai tantance bukatar tafiye-tafiye

Wannan sabuwar dokar, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito, za ta taimaka wajen rage kudin tafiyar da mulki da gwamnati ke yi.

Tinubu ya kara da cewa jami'an gwamnati da ke son fita waje domin aikin gwamnati, za su nemi amincewar shugaban kasar kai tsaye.

Har sai shugaban Najeriyan ya ga dacewar tafiyar ne zai amince da hakan, kuma dole a sanar da shi makonni biyu kafin ranar yin tafiyar.

Ministan Tinubu na fuskantar tuhuma

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar wakilai za ta fara gudanar da bincike kan ma'aikatar ilimi domin gano yadda aka kashe $300m na yaki da zazzabin cizon sauro.

Majalisar ta gayyaci ministan lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate da ya gurfana gabanta domin amsa tambayoyi kan wannan badaƙalar kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel