Akwai Alamun Samun Sauƙi, Darajar Naira Ta Lula Zuwa N1400/$1 a Kasuwar Canji

Akwai Alamun Samun Sauƙi, Darajar Naira Ta Lula Zuwa N1400/$1 a Kasuwar Canji

  • Naira ta samu gagarumar nasara a kasuwar canji a ranar Laraba, inda darajarta ta lula sama zuwa N1,410/$1 a kasuwar hada-hada
  • A kasuwar bayan fage kuwa, Musa Lawal Bakori, a zantawarsa da Legit Hausa, ya ce suna sayen $1 a kan N1,400 suna sayarwa a kan N1,450
  • Faduwar darajar dalar Amurka, na zuwa ne bayan da bankin CBN ya sanar da cewa ya kammala biyan bashin $7bn da ake binsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Naira ta samu daraja sosai a kasuwar canji ta gwamnati da ma ta bayan fage a ranar Laraba biyo bayan faɗuwar darajar dalar Amurka.

Matakin da CBN ya dauka ya daga darajar Naira zuwa N1400/$1
An yi cinikin $1 akan N1,410 a kasuwar hada-hada, da kuma N1,492/$1 a kasuwar NAFEM. Hoto: @Yemi_Card
Asali: Facebook

CBN ya kammala biyan bashin $7bn

Wannan na zuwa ne bayan da babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da kammala biyan duk wani bashi na kudin waje da ake binsa.

Kara karanta wannan

Ana sa ran naira za ta mike, CBN ya biya bashin Dala biliyan 7 da Emefiele ya bari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mr. Olayemi Cardoso, gwamnan CBN, ya ce ya gaji bashin $7bn da ake bin bankin, amma yanzu ya kammala biya gaba daya.

Talabijin na Arise ya ruwaito cewa mukaddashiyar daraktar CBN, bangaren hulda da jama'a, Mrs. Hakama Sidi Ali, ta bayyana hakan a Abuja.

Idan muka duba kasuwar canji a ranar Laraba, za mu ga cewa an yi cinikin $1 a kan N1,410 a kasuwar hada-hada, yayin da ta ke N1,492/$1 a kasuwar NAFEM.

Menene dalilin faduwar darajar Dala?

Bayanan da aka samu daga shafin Businessday sun nuna cewa a ranar Talata 19 ga watan Maris, Naira ta kara daraja zuwa N1,583/$ a kasuwar NAFEM da misalin karfe 12:57 na rana.

Kamar yadda binciken jaridar The Punch ya nuna, darajar Naira ta haura sama ne sakamakon sayar da dalar Amurka da ake yi ba ƙaƙƙautawa, biyo bayan wasu matakai na CBN.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta bankaɗo kura-kurai a bashin N30tn da CBN ya ba gwamnatin Buhari

Matakai da dama da CBN ya dauka a makonni da watannin da suka gabata sun taimaka wajen dakile masu boye daloli da masu tsawwala farashin kudin.

Haka zalika, kamen ƴan canji (BDC) da hukumomin yaƙi da rashawa suka yi a Legas, Abuja da Kano ya taimaka wajen hawa da saukar farashin Naira.

N1400/$: Abin da ƴan canji ke cewa

Wani ɗan canji a Legas, Musa Lawal Bakori, wanda ya zanta da Legit Hausa a ranar Alhamis, ya ce farashin $1 a kasuwar ƴan canji ya sauka zuwa kasa da N1,500.

Ya ce a yanzu suna sayen dalar Amurka a kan N1,350 zuwa N1,400 sannan suna sayar wa N1450, wasu lokutan sama da hakan idan kayan na da yawa.

Ko da aka tambaye sa abin da ya ke gani kan matakan gwamnati da CBN na karya farashin dala, Bakori ya ce:

"Matakai ne masu kyau, ko ba komai zai taimaka mana wajen samuwar dalar cikin sauki, domin har yanzu tana wahala a kasuwar."

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojojin Najeriya sun halaka wani shugaban ƴan bindiga da mayakansa

A hannu daya kuma, an samu karuwar hada-hadar kudi da kusan $268.29 daga $195.13 da aka samu a ranar Talata.

Dabarun CBN sun taimaka wa Naira

A baya-bayan nan, Legit Hausa ta ruwaito cewa dabarun da babban bankin Najeriya (CBN) ya ke amfani da su sun taimaka wajen farfaɗo da darajar Naira.

Idan ba a manta ba, a makon karshe na watan Fabrairu, Naira ta yi faduwar da ta girgiza abokan ciniki, inda ta kusa haura N2,000/$1.

Asali: Legit.ng

Online view pixel