Jami’an EFCC Sun Kai Samame Wurin ’Yan Canji a Kano, Abuja da Oyo Akan Wani Dalili 1 Tak

Jami’an EFCC Sun Kai Samame Wurin ’Yan Canji a Kano, Abuja da Oyo Akan Wani Dalili 1 Tak

  • Jami'an hukumar EFCC sun kai sumame kasuwar 'yan canjin kudi ta WAPA da ke jihar Kano, inda suka kama mutane da dama
  • Tun kafin wannan sumamen, Legit Hausa ta ruwaito yadda jami'an hukumar suka kama 'yan canjin kudi a jihohin Oyo da birnin Abuja
  • Wannan na zuwa ne bayan da Mallam Nuhu Ribadu, ya bayar da umarnin daukar mataki kan masu haifar da tashir farashin dala

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta kama wasu masu gudanar da canjin kudi a shahararriyar kasuwar canji ta WAPA da ke jihar Kano.

A cewar wani ganau, Malam Isma’ila Zico, jami’an hukumar EFCC sun je kasuwar ne a safiyar ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban labari: EFCC ta cafke 'yan canji a Abuja, an gano dalili

Jami’an EFCC suna ci gaba da kai samame wurin ‘yan canji
Jami’an EFCC suna ci gaba da kai samame wurin ‘yan canji don dakile faduwar darajar Naira. Hoto: EFCC
Asali: UGC

Yadda jami'an EFFC suka kai sumame WAPA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zico ya labarta cewa:

“Sun yi amfani da kwarewa wajen gudanar da aikin, bayan kamen ne muka gano cewa tun safe suke a kasuwar ba tare da kowa ya lura ba.
"Har sai a lokacin da za su fara kamen ne muka ga jami’ansu sanye da rigunan hukumar da wasu jami’an tsaro, inda suka kewaye sashen canjin dala na kasuwar."

Sai dai ya ce ba zai iya shaida adadin mutanen da jami'an suka kama a kasuwar ba.

Shugaban kasuwar canjin kudi ta WAPA ya magantu

Da aka tuntubi shugaban kasuwar canjin kudi ta WAPA, Alhaji Sani Salisu Dada, ya tabbatar da wannan samame.

Dada ya kara da cewa jami’an hukumar ta EFFC sun je kasuwar ne domin shawo kan matsalar tabarbarewar Naira da ake zargin 'yan canji na haddasawa a kasuwar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan bindiga a Arewa, sun kwato muggan makamai

Ya bayyana cewa EFCC ta kama wasu 'yan canji a lokacin kuma an tafi da su don ci gaba da bincike.

Shugaban ya kara da cewa tuni daka dawo da hada-hada a kasuwar kuma kungiyar a shirye take ta bida hadin kai idan bukatar hakan ta taso.

EFCC ta kama 'yan canji 10 a Sabo, jihar Oyo

Daily Post ta ruwaito cewa jami’an hukumar EFCC sun kuma kai samame kan 'yan kasuwar canji da ke Sabo, Ibadan, bisa zargin karin kudin canjin naira da dala.

Wani ganau da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama akalla mutane goma, sannan jami’an sun kwace makudan kudade.

Ya kuma tabbatar da cewa a halin yanzu ana yin cinikin dala 1 a kasuwar kusan akan naira 1900 zuwa naira 1,940.

EFCC ta kai samame Wuse Zone 4, Abuja

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, jami'an hukumar EFCC sun kai samame a kasuwar BDC da ke Wuse Zone 4, Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya bayar da umarnin daukar matakan dakile masu haifar da tashir farashin dala da boye kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel