CBN Ya Dauki Mataki Mai Karfi Domin Farfado da Darajar Naira A kan Dalar Amurka

CBN Ya Dauki Mataki Mai Karfi Domin Farfado da Darajar Naira A kan Dalar Amurka

  • Bankin CBN ya kuduri aniyar lalubo hanyoyin magance matsalolin Naira, inda a ‘yan makonnin nan ya dauki muhimman matakai
  • A baya-bayan nan bankin ya siyar da takardun kudin baitul-mali ga 'yan kasuwa na kasashen waje da nufin kara yawan kudinta a kasuwar FX
  • Darajar kudin Najeriya a cikin kwanaki biyun da suka gabata ta fara sauka kasa a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, lamarin da ya girgiza CBN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Babban bankin Najeriya ya yi nasarar sayar da wasu takardun kudin baitul-mali na Naira tiriliyan 1.3 ga masu zuba jari na kasashen waje (FPI) a ranar Laraba, 6 ga Maris, 2024.

Babban bankin Najeriya (CBN )
CBN zai yi amfani da N1.3tn don daga darajar Naira. Hoto: CBN, Getty Image
Asali: UGC

Wannan dai na daya daga cikin kokarin da CBN yake yi na farfado da Naira, wanda darajar ta ke faduwa a kasuwannin hannayen jari sakamakon karancin ta.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara binciken gwamnatin Buhari kan kashe N200b a shirin kidayar 2023 da aka dakatar

Ta ya ake lissafin takardun kudin baitul-mali?

Rahoton bankin Stanbic ya nuna cewa CBN ce ke fitar da takardun kudin baitul-mali, wanda kuma aka fi sani da T-Bills, a duk lokacin da gwamnati ke bukatar amfani da manyan kudade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, bankin na amfani da 'T-Bills' a lokutan da gwamnati ke bukatar aro kudi na gajeren lokaci. Bankin na iya amfani da takardar kudin ne na tsawon kwanaki 364.

Business Day ya rahoto yadda CBN ke sayar da takardun kudin baitul-malin ta hanyar yin gwanjonsu a mako-mako. Masu saye za su gabatar da farashinsu, inda a karshe ake sayar wa mai matsakaicin farashi.

Yadda aka yi gwanjon takardun kudin a baya

Gwamnati na siyar da wadannan takardun kudin a kan farashi mai sauki (kudin ajiya). Amma bayan kamar shekara daya, sai gwamnati ta biya mutane kudin takardun na gaskiya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000? An bankado shirin wasu mazambata

A cewar rahoton Business Post, CBN ya shigar da takardun kudin kasuwa tare da neman N312.9b don ajiyar kudin na kwanaki 364, amma ta samu karin darajar kudin zuwa N1.5tn daga hannun masu zuba jari.

Babban bankin na CBN zai yi amfani da kudaden da ya samu a wajen gwabzawa da dala a kasuwar hada-hadar kudi da kuma maido da canjin kudin zuwa kasa da N1,500/$.

CBN ya dawo cigaba da saida daloli ga BDC

A wani labarin, babban bankin Najeriya CBN, ya ci gaba da sayar wa masu harkar cinikin kudin kasashen waje (BDC) daloli da nufin daga darajar Naira da karya dalar.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, bankin ya yanke shawarar ba kowane dan canji da ke da rijista da bankin $20,000 kuma za ta bada duk $1 a kan N1,301.

Asali: Legit.ng

Online view pixel