Ramadan: Gwamnan APC Ya Ware N6.7bn Domin Rabawa Marayu da Talakawa Tallafin Azumi

Ramadan: Gwamnan APC Ya Ware N6.7bn Domin Rabawa Marayu da Talakawa Tallafin Azumi

  • Gwamnatin jihar Sakkwato ta ware N6.7bn domin ciyar da marasa ƙarfi a watan azumin Ramadan wanda aka fara ranar Litinin
  • Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana haka a wurin taron kaddamar da rabon hatsi ga marayu da gajiyayyu 18,400
  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, ya yabawa gwamnan bisa ci gaba da shirin ciyarwa tare da tabbatar masa da goyon bayansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato da ke shiyyar Arewa maso Yamma ta ce ta ware zunzurutun kuɗi N6.7bn domin ciyar da mutane masu ƙaramin ƙarfi a watan Ramadan.

Wannan shirin ciyarwa a watan Ramadan na gwamnatin Sakkwato ya ƙunshi raba hatsi kyauta ga talakawa da kuma rabon abinci a cibiyoyin ciyarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince zai raba tallafin abinci ga talakawa sama da miliyan 2 a Ramadan

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato.
Marayu, gajiyayyu da talakawa za su samu tallafi a jihar Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da rabon hatsi ga marayu 18,400 da gajiyayyu a fadin jihar Sakkwato, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kowanne mutum ɗaya daga cikin marayu 18,400 da gajiyayyu zai karbi tallafin buhunan shinkafa da gero da kuma tsabar kudi Naira 5,000.

Sarkin Musulmi ya gode wa gwamnan Sakkwato

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya gode wa gwamnatin jihar kan yadda ta ci gaba da gudanar da shirin ciyar wa a watan Ramadan.

Sarkin Musulmin ya kuma bai wa Gwamnan Ahmed Aliyu tabbacin goyon bayansa a kokarinsa na inganta rayuwar jama’a musamman a wannan lokacin.

A rahoton Vanguard, Sultan na Sakkwato ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tausaya wa mabukata a wannan wata na Ramadan duba da halin ƙuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

A ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024, musulmin Najeriya suka fara azumin watan Ramadan bayan Sarkin Musulmin kasar ya sanar da ganin jinjirin wata.

Gwamnatin Katsina ta ware N10bn a Ramadan

Tun kafin haka gwamnatocin jihohi musamman a Arewa suka fara shirye-shiryen tallafawa mutane duba da halin tsadar rayuwa da yunwar da ake ciki.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, na ɗaya daga ciki, ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta sayar da buhunan masara, gero da dawa a farashi mai sauƙi.

Ya kuma kaddamar da kwamitin da zai jagoranci ciyar da talakawa marasa ƙarfi sama da miliyan biyu a wannan wata mai albarka

Ramadan: Babban abin da Najeriya take buƙata

A wani rahoton kuma Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya bi sahu wajen taya al'ummar musulmai murnar zuwan watan azumi na Ramadan.

Abbas ya kuma buƙaci ƴan Najeriya su sa ƙasar nan cikin addu'a domin fitowa daga cikin halin ƙalubale da matsalolin da take fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel