Sharo: Saurayi ya rasa ran sa wajen neman aure
- Samarin Fulani sai sun nuna bajinta kafin su sami matar aure
- Saurayi ya shiga sharo don ya nuna bajinta, ya rasa ran sa
- 'Yan-sanda sun damke abokin hamayyar
Wani saurayi, Yari Inusa, ya rasa ransa a gasar Sharo da ya shiga don neman auren wata budurwa. Wannan ya faru ne a kauyen Durumin Biri dake karamar hukumar Kafur a Jihar Katsina.
'Yan-sanda sun ce Inusa ya rasa ransa ne bayan abokin karawarsa, Ahmad Sa'idu, ya dake shi a ka da bulala a yayin da suke gasar.
Sharo al'adar Fulani ce wanda in samari biyu suka nemi auren budurwa daya, sai a basu fili suyi jibgar junan su a baya da tsimammun bulali har sai rago ya baiyana a cikin su. Budurwa kuma sai ta auri wanda ya fi gwarzanci.
Inusa ya jibgi Saidu kalau, amma da aka kawo kan Sa'idu, sai ya yiwa Inusa a ka. Nan take Inusa ya suma, kuma bada jimawa ba da hakan ya ce ga garinku.
DUBA WANNAN: Manoma na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara
Mai magana yawun 'yan-sandan Jihar Katsina, DSP Gambo Isah, ya gaskata wannan ta'asa.
Yace, "Mahaifin Inusa ya kawo mana karar wannan al'amari, mu kuma mun je mun damki Sai'du. A yanzu haka yana hannun mu."
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng