Ramadan: Gwamnan Arewa Ya Tausaya, Zai Tallafawa Mutum 171,900 Kowace Rana a Watan Azumi

Ramadan: Gwamnan Arewa Ya Tausaya, Zai Tallafawa Mutum 171,900 Kowace Rana a Watan Azumi

  • Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce zai ciyar da mutane 171,900 a kowace rana a watan azumin Ramadana da ke dab da shigowa
  • Ɗanmodi ya ce gwamnatin ta kafa cibiyoyi biyu a kowace gunduma domin rabawa mutane abinci tun azumin farko har zuwa na ƙarshe
  • Kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Sankara ya ce akalla mutum 5 ake sa ran zasu amfana da tallafin kayan abinci daga kowane gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ciyar da mutane 171,900 a kullum a cikin watan azumin Ramadan mai zuwa nan da wasu ƴan kwanaki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da rabon kayan tallafin abinci ga mazauna garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamna a Arewa ya tausaya, zai raba tirelolin abinci 200 kyauta domin rage wahala

Gwamna Umar Namadi.
Ramadan: Jigawa Za Ta Ciyar da Mutum 171,900 Kowace Rana – Gwamna Namadi Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Ɗanmodi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tsara ciyar da mutane ƴan asalin jihar Jigawa 5,157,000 a tsawon watan Ramadan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa ya kafa cibiyoyi biyu a kowace gunduma da ke faɗin jihar domin aiwatar da shirin cikin nasara.

Yadda gwamnan ya kafa cibiyoyi a kusa da talakawa

Ya kara da cewa, ana sa ran kowace cibiya za ta ciyar da akalla mutane 300 a kullum, wanda ya kai adadin 171,900 a kowace rana idan aka haɗa jimullar cibiyoyi 573.

Gwamnan ya ce wannan shiri ya wuce ciyar da talakawa a wuraren da jama’a ke taruwa kaɗai, inda ya kara da cewa an sanya magidanta a cikin tsarin.

Umar Namadi ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta kirkiro shirin ciyarwan ne domin tallafawa mabuƙata a watan azumin Ramadan mai albarka da tarin yafiya.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas ya fadi abin da ya yi niyya lokacin shirin tsige shi

Gwamnan ya kuma yi alkawarin sake shirya raba tallafin wanda Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi alkawari ga al’ummar Jigawa, cewar rahoton Pulse.

Bisa haka ya tabbatar wa mazauna Jigawa cewa gwamnatinsa ta shirya share masu hawaye musamman a halin tsadar rayuwar da ake ciki a kasar nan.

Ramadan: Jigawa zata raba buhunan shinkafa

Tun da farko, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwalu Sankara, ya ce za a raba buhunan shinkafa 25,000, buhunan masara 150,000 da katan-katan na spaghetti 100,000 ga magidanta 150,000.

Sankara ya ce gwamnatin ta yi tanadi ga mutane 700,000 da zasu ci gajiyar tallafin a kananan hukumomin jihar 27, kuma ana sa ran mutum 5 zasu amfana a kowane gida.

Sarkin Musulmi ya bada umarnin a duba wata

A wani rahoton kuma Mai alfarma sarkin musulmi a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar na III, ya buƙaci a fara duban jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da majalisar ƙoli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA) ta fitar ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel