Dalilan dake jawo kulluwar abota ko kawance tsakanin mace da namiji

Dalilan dake jawo kulluwar abota ko kawance tsakanin mace da namiji

Ana ci gaba da cece-kuce a kan kulla alaka tsakanin mace da namiji bada niyyar soyayya ko aure ba, sai don kawai kawance ko kuma abota. Wanne kallo kuke yiwa kawance ko abota tsakanin namiji da mace?

Naijcomhausa tayi nazarin wasu dalilai dake kawo kulkuwar alaka tsakanin namiji da mace da har take kaisu ga zama abokan juna.

1. Tasowa tare: Mace da namiji kan iya samun shakuwa kasancewar sun taso tare tun daga yarinta. Yana iya kasancewa sun taso gida daya, unguwa daya, ko kuma sun halarci makaranta daya.

Dalilan dake jawo kulluwar abota ko kawance tsakanin mace da namiji
Dalilan dake jawo kulluwar abota ko kawance tsakanin mace da namiji

2. Hali yazo daya: A wasu lokuta mutum ya kan hadu da wani ko wata da ra'ayinsu yazo iri daya, sai kaga tun daga lokacin da suka hadu sun samu shakuwar da zata kaisu sun zama abokan juna, amma kuma ba wai suna soyayya bane. Irin wannan haduwa na iya faruwa ta hanyar karatu, aiki, kasuwa da sauransu.

3. 'Yan uwantaka: Namiji da mace suna iya yin sabo matuka da juna kasancewarsu 'yan uwan juna. 'Yan uwantaka na iya haifar da kauna mai karfi tsakanin namiji da mace.

DUBA WANNAN: Warware zare da abawa tsakanin rikicin gwamnatin tarayya da kamfanin Intels na Atiku

4. Baiwa ta musamman: Wasu mutane, maza da mata, ALLAH na iya yi masu wata baiwa ta ilimi, barkwanci, lafazi da sauransu da zaka ga da yawan mutane na son kulla abota da su. Mace ko namiji ko mai irin wannan baiwa zaka sun samu abokai daga dukkan jinsin mace ko namiji.

5. Yanar gizo-gizo: Shakka babu sabuwar fasahar zamani ta yanar gizo-gizo ta kawo hanya mai sauki ta sada zumunta da kulla abota tsakanin mutane. Abota ko kawance tsakanin namiji da mace kan iya kulluwa ta dalilin musayar ra'ayi ko mahawara a dandalin sada zumuntar zamani.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel