Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 10 a Titin Kaduna Zuwa Abuja

Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 10 a Titin Kaduna Zuwa Abuja

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin dinnan
  • Hatsarin ya ritsa ne da wata babbar motar tirela wacce ta ƙwacewa direbanta sannan ta faɗa cikin wani rami
  • Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa ta tabbatar da lamarin ta ce mutum 10 ne suka rasa ransu yayin da wasu mutum 48 suka samu raunuka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ce fasinjoji 10 ne suka mutu a ranar Litinin a wani hatsarin mota.

Hukumar ta ce hatsarin motan ya ritsa da wata babbar motar tirela ne kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, za ta dauki mataki

An yi hatsarin mota a titin Abuja/Kaduna
Hatsarin mota a titin Abuja/Kaduna ya salwantar da rayukan mutum 10 Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Jami’in hulɗa da jama'a na hukumar, Jonas Agwu, ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri, ɗauko kaya masu yawa da kuma gajiya, rahoton jaridar Premium Times.

Me ya haddasa hatsarin?

A cewarsa, direban motar ta ƙwace masa ne, inda ya faɗa cikin wani rami da misalin ƙarfe 10:30 na safe ɗauke fasinjoji maza mutum 172 a cikin tirelar.

Mista Agwu ya ce mutum 10 daga cikin fasinjojin sun mutu yayin da mutum 48 suka samu raunuka.

Ya ce, hukumar ta FRSC ce ta kai waɗanda hatsarin ya ritsa da su zuwa asibitocin St. Anthony da Umaru Musa Yar’adua da ke Kaduna.

Jami'in ya ƙara da cewa:

"Hukumar FRSC na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa waɗanda suka jikkata da ke kwance a asibitoci sun samu kulawar da ta dace."

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Mista Agwu ya ambato shugaban hukumar ta FRSC, Dauda Ali-Biu, yana kira ga kwamandojin shiyya-shiyya da su su ci gaba da wayar da kai a ƙasa baki ɗaya kan illar gudun wuce gona da iri, ɗauko kaya masu yawa da tuƙin ganganci.

Mutum 12 sun mutu a hatsarin mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa na samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Hatsarin wanda ya ritsa da wata motar tirela ya salwantar da rayukan mutum 12 ciki har da direbanta, yayin da wasu mutum 28 suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel