Tsadar Rayuwa: Kashim Shettima Ya Magantu Kan Yunwa a Kasa, Ya Fadi Muhimmin Abin da Tinubu Ke Yi

Tsadar Rayuwa: Kashim Shettima Ya Magantu Kan Yunwa a Kasa, Ya Fadi Muhimmin Abin da Tinubu Ke Yi

  • Kashim Shettima, mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ƙara da cewa ƙasar na kan hanyar samun ƴanci
  • Shettima ya ce ya ga zuciyar Shugaba Tinubu kuma yana nufin alheri ga ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa abin da ke faruwa a yanzu shi ne illar fallasa miyagu
  • A cewar mataimakin shugaban ƙasan, cire tallafin man fetur ya sa shafaffu da mai suka riƙa kawo cikas, amma ya yi amanna cewa cewa ƙasar nan na kan turbar dawowa daidai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi hakuri da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ƴan sanda sun bayyana mummunan laifin da ya sa aka kama shugaban LP na ƙasa

Mataimakin shugaban ƙasan ya ƙara da cewa ya ga zuciyar shugaban ƙasan kuma yana da tsaftatacciyar zuciya.

Shettima ya fadi halin Tinubu
Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da Tinubu Hoto: Kashim Shettima, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan matsalar yunwa a ƙasar nan, inda ya bibiyi yadda aka cire tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya yi nuni da cewa lokacin bada tallafin man fetur ya sanya wasu mutane tsiraru a ƙasar nan sun azurta kansu da dukiyar talakawa.

A cewar Shettima, abin da ke faruwa a ƙasar nan a halin yanzu shi ne illar fallasa wata ɓarna a cikin jama’a, wanda shi ne cire tallafi, amma a wajensa Najeriya na kan turbar dawowa daidai.

Ya ce ya kamata jama’a su yi haƙuri da shugaban ƙasa kan halin da ake ciki domin yana nufin alheri ga ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Ina ji a jika": Tsohon gwamna ya koka kan daurin da EFCC ta yi masa

Shettima ya yi magana yayin da ake zanga-zanga a ƙasa

Kalaman mataimakin shugaban kasar na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya da dama suka koka kan yadda ake fama da yunwa a ƙasar nan.

A wasu jihohin wasu sun gudanar da zanga-zanga.

Wani ɓangare na bayanin nasa na cewa:

"Ɗaya daga cikin baƙar fata guda huɗu ɗan Najeriya ne, kuma nan da shekarar 2050, Najeriya za ta zama ƙasa ta uku a yawan al’umma a duniya, za mu wuce Amurka.
"Ɗaya daga cikin kowane ƴan Afirka uku zai zama ɗan Najeriya. Dole ne mu sanya ƙasar nan aiki. Ya kamata mu wuce siyasa."

Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma yi tir da gwamnonin da aka zaba a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP saboda kwatanta tattalin arzikin Najeriya da na Venezuela.

Dalung Ya Taso Tinubu a Gaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan matasa da wasanni a gwamnatin Buhari, ya caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Solomon Dalung ya bayyana cewa ya kamata shugaban ƙasan ya farka ya daina ɗora alhakin halin da ake ciki a ƙasar nan a kan gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel