Abin Farin Ciki Yayin da Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe 2 Masu Muhimmanci a Ramadan

Abin Farin Ciki Yayin da Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe 2 Masu Muhimmanci a Ramadan

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe domin gyara tawagar shugabannin hukumar almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta
  • Shugaban ƙasar ya naɗa Birgediya Janar Lawal Ja'afar Isa (mai ritaya) a matsayin sabon shugaban majalisar da ke kula da hukumar almajirai
  • Da farko an naɗa Jafaru Isah a matsayin babban sakatare/shugaba kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya ɗaga shi zuwa gaba a ranar Litinin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabuwar tawagar waɗanda za su jagoranci hukumar kula da almajiri da yaran da ba su zuwa makaranta.

Tinubu ya amince da naɗin Birgediya Janar Lawal Ja'afaru Isah (mai ritaya) a matsayin babban shugaban hukumar ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya fara shirin korar wasu Ministoci daga aiki, ya jero matakai 3

Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya yi gyara a naɗe-naɗen hukumar almajiri Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya kuma nada Dakta Muhammad Sani a matsayin babban sakataren hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin, 18 ga watan Maris, 2024.

Fredrick Nwabufo, mai taimakawa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai ne ya wallafa wannna sanarwa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

A sanarwar, shugahan kasa Tinubu ya buƙaci waɗanda aka naɗa da su zube dukkan basira da kwarewar da Allah SWT ya masu wajen sauke nauyin da ke kansu.

Wanene Birgediya Janar Ja'afaru Isa mai ritaya?

A farko, shugaban Tinubu ya naɗa Birgediya Janar Ja'afaru Isa a kujerar babban sakatare/shugaban hukumar almajirai amma daga bisani ya ɗaga shi zuwa matakin shugaba.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Yanzu dai Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (Rtd) ne zai zama shugaban hukumar yayin da Dakta Idris Muhammad Sani zai zama babban Sakatare/Shugaba."

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

Janar Ja’afaru Isa jigo ne da ake mutuntawa kuma ya taba rike mukamin hakimin soja watau gwamna a mulkin sojoji na jihar Kaduna daga 1993 zuwa 1996.

Edo 2024: Tinubu ya yi hasashen nasarar APC

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi hasahen cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a watan Satumba, 2024.

Shugaban ƙasa ya kuma miƙa tutar APC ga ɗan takarar gwamna, Sanata Monday Okpebholo, da abokin gaminsa, Honorabul Dennis Idahosa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel