Gwamna Ya Fadi Halin Kunci da Ya Ke Ciki, Ya Ce Shekaru 2 Bai Samu Albashi Ba, Ya Yi Tone-tone

Gwamna Ya Fadi Halin Kunci da Ya Ke Ciki, Ya Ce Shekaru 2 Bai Samu Albashi Ba, Ya Yi Tone-tone

  • Gwamnan jihar Anambra ya fadi gaskiya kan halin da ya ke ciki a jihar ba tare da karbar albashi ba na tsawon shekaru
  • Gwamnan Charles Soludo ya ce ya shafe shekaru biyu ba tare da samun albashi daga gwamnatin jihar ba
  • Ya kara da cewa ko matarsa ba ta da motar shiga da gwamnatin ta bata sai dai ta yi amfani da motocinsa da ya ke da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ya shafe shekaru biyu ba tare da albashi ba.

Soludo ya kara da cewa matarsa ko mota ba ta da shi sai dai ta na yin amfani da motocinsa, cewar Nairametrics.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Gwamna a Najeriya ya bayyana halin kunci na rashin kuɗi da ya ke fama da shi
Gwamna Soludo na Anambra ya ce ya shafe shekaru 2 bai karbi albashi ba. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

Halin da jihar Anambra ke ciki na rashin kudi

Gwamnan ya bayyana haka ne yau yayin bikin cika shekaru biyu a kan mulki a birnin Awka da ke jihar, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk wani gwamna da zai zo maka da maganar basuka da wasu abubuwa, amma mun yanke shawarar yin abin da ya dace da ɗan abin da muke da shi."
"An yawan tambaya ta, ya kake gudanar da mulki babu basuka, abin da nake fada shi ne muna daukar matakai ne masu tsauri."
"A yanzu da nake magana da ku, ba a biya na albashi, gwamnatin jihar Anambra bata biya na, uwar gida na ba ta da mota a hukumance, ta na amfani ne da motocina."

- Charles Soludo

Soludo ya gargadi shugaban karamar hukuma

Har ila yau, Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya caccaki wani ciyaman na karamar hukuma, Pascal Aniegbuna kan rashin kula da aikinsa.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin abinci, Gwamnan APC ya lissafo kasuwannin da za a iya samun kayan cikin sauki

An gano gwamnan a cikin wani faifan bidiyo ya na cin mutuncin ciyaman din a cikin taron jama’a a kasuwa.

Gwamna Adeleke ya shiga gidan gwamnati

A baya, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tare a gidan gwamnatin jihar bayan karbar rantsuwar kama mulki.

Gwamnan akalla ya shafe shekara daya da watanni hudu a gidansa na ainihi ba tare da shiga gidan gwamnatin ba.

Gwamnan ya karbi rantsuwa ne a matsayin gwamnan jihar tun a ranar 27 ga watan Nuwambar 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel