Tinubu Ya Ba da Sabon Umarni Ga Rundunar Tsaro Bayan Kisan Sojoji 16, Ya Yi Allah Wadai

Tinubu Ya Ba da Sabon Umarni Ga Rundunar Tsaro Bayan Kisan Sojoji 16, Ya Yi Allah Wadai

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan sojoji 16 a kauyen Okuama da ke jihar Delta a Kudancin Najeriya
  • Tinubu ya nuna bacin ransa inda ya umarci rundunar tsaron kasar da ta tabbatar ta zakulo wadanda ake zargi
  • Wannan na zuwa ne bayan hallaka jami'an sojoji akalla 16 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi martani kan kisan sojoji 16 da aka yi a wani kauye da ke jihar Delta.

Tinubu ya ba hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa umarnin zakulo wadanda ke sa hannu a kisan tare da hukunta su.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Gwamnan PDP ya yi martani kan harin, ya fadi abin da zai yi kan lamarin

Tinubu ya yi martani kan kisan sojoji 16 a jihar Delta
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan sojoji 16 a kauyen jihar Delta. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Martanin Tinubu kan kisan sojojin a Delta

Har ila yau, shugaban ya ba da umarnin makamancin wannan ga hedkwatar tsaron da ke birnin Abuja domin bincike mai tsauri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da sanya wa hannu a yau Lahadi 17 ga watan Maris.

Ya ce kai hari kan jami'an sojoji kamar aiwatar da hari ne kan kasar baki daya inda ya ce ba zai lamunci haka ba a mulkinsa.

Ya kuma tura sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da abokan aikinsu da kuma masoyansu baki daya.

Alkawarin da Tinubu ya dauka kan lamarin

"Wannan lamari ya sake tabbatar da hatsarin da jami'an tsaronmu mata da maza ke fuskanta a ƙasar."
"Na yabawa jami'anmu wurin jajircewa da aiki tukuru, a matsayinmu na kasa dole mu mutunta wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare Najeriya."

Kara karanta wannan

Bayan kisan sojoji 16, an bankawa kauyen da abin ya faru wuta, bayanai sun fito

"Jami'an da suka mutu a Okuama sun shiga sahun wadanda suka rasa rayukansu wurin kare mutuncinmu."
"Gwamnati na ba za ta gajiya ba har sai ta tabbatar da zaman lafiya a Najeriya."

- Bola Tinubu

Fusatattun sojoji sun dauki mataki

Kun ji cewa ana zargin wasu sojojin sun kona kauyen da aka hallaka sojoji 16 a wani kauyen jihar Delta.

Wannan na zuwa ne bayan hallaka sojoji 16 sa wasu bata gari suka yi a kauyen Okuama a karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel