Cire Tallafin Mai: Matsaloli Hudu Da 'Yan Najeriya Ke Fama Da Su Bayan Cire Tallafin

Cire Tallafin Mai: Matsaloli Hudu Da 'Yan Najeriya Ke Fama Da Su Bayan Cire Tallafin

Sanar da cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi a lokacin jawabinsa na farko wajen rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, ya sanya matsaloli da yawa sun auku a ƙasar nan.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sai dai, Tinubu a jawabin nasa ya bayyana dalilin daina biyan tallafin shi ne gwamnatin magabacinsa Muhammadu Buhari, ba ta sanya biyan tallafin ba a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023.

Matsalolin da cire tallafin man fetur ya janyo
Shugaba Tinubu dai yana hawa mulki ya sanar da cire tallafin Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Yadda cire tallafin man fetur ya shafi rayuwar ƴan Najeriya

A halin da ake ciki yanzu cire tallafin man fetur ɗin ya janyo tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki a ƙasar nan, inda masu kuɗi da talakawa kowa ke ji a jikinsa.

Legit.ng ta tattaro matsalolin da ke damun ƴan Najeriya da suka ɓullo bayan gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

El-Rufai, Ganduje, Da Wasu Tsofaffin Gwamnoni 4 Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Nada Minista

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Tashin farashin man fetur

Sa'o'i kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi daga N195 zuwa N490, N500 kan kowace lita a jihohin ƙasar nan.

Ƴan Najeriya na shan wuya a halin yanzu, sannan tashin farashin man fetur ɗin ya ƙara tsadar kayan abinci da kuɗin mota.

2. Ƙarin farashin kayayyaki

An samu sauyin farashin kayayyakin da ake amfani da su a kasuwanni. A kasuwanni da dama farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zaɓi.

3. Tashin kuɗin mota

Cire tallafin man fetur ɗin ya janyo kuɗin zirga-zirga a motar haya sun ƙaru sosai a ƙasar nan.

Yanzu haka kusan kuɗin motar sun ninka ne kan yadda a baya aka saba ana biya. Tafiyar da ada aka saba ana biyan N100, N200 yanzu ta koma sai an biya N300, N400.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Tonon Silili Kan Dalilin Da Ya Sanya Yake Nade-Naden Mukamai

4. Tsadar Rayuwa

Tsadar rayuwa ta ƙaru wanda hakan ya sanya rashin aikin yi ya ƙaru sosai a tsakanin ƴan Najeriya.

Kuɗin wutar lantarki, kuɗin haya da sauransu duk sun ƙaru yayin da kusan rabin ƴan Najeriya basu da aikin yi mai gwaɓi ko basu da aikin yin ma gaba ɗaya.

Sai dai, ana sanya ran cewa shugaban ƙasar zai shawo kan wannan matsalar ta ragu sosai domin ceto al'ummar ƙasar daga halin da suka tsinci kansu a ciki.

Yawan Shan Man Fetur Ya Ragu a Najeriya

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yawan man fetur ɗin da ake amfani da shi a ƙasar nan ya yi ƙasa sosai.

Gwamnatin tarayyar ta koka da cewa yawan man fetur ɗin da ake sha ya ragu da kusan lita miliyan 18.5 a wata ɗaya kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel