Kamfanonin Simintin Dangote Da BUA Sun Kashe Kudi N205bn Kan Siyan Man Fetur Cikin Watanni 6

Kamfanonin Simintin Dangote Da BUA Sun Kashe Kudi N205bn Kan Siyan Man Fetur Cikin Watanni 6

  • Kamfanonin siminti na Dangote da BUA sun bayyana irin makudan kudade da su ka kashe kan samar da wutar lantarki a ma’aikatunsu
  • Sun bayyana cewa akalla sun kashe makudan kudade har Naira biliyan 204.925 a cikin watanni shida na wannan shekara da muke ciki
  • An samu karuwar kashi 18 idan aka kwatanta da Naira biliyan 175.537 da kamfanonin su ka kashe a shekarar 2022

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Manyan kamfanonin siminti biyu a Najeriya, Dangote da BUA sun bayyana yadda su ke kashe makudan kudade don samar da wutar lantarki ga kamfanonin.

Dangote da BUA sun bayyana cewa sun kashe kusan Naira biliyan 204.925 a cikin watanni shida na wannan shekara da muke ciki, Legit.ng ta tattaro.

Kamfanonin siminti na Dangote da BUA na kashe N204bn kan siyan man fetur
Kamfanonin Siminti Na Dangote Da BUA Sun Bayyana Yawan Kudaden Da Su Ke Kashewa Kan Man Fetur. Hoto: Bloomberg / Contributor.
Asali: Getty Images

Hakan ya karu da kashi 18 idan aka kwatanta da Naira biliyan 175.537 da su ka kashe a cikin watanni shida na shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Orire Agbaje: Bayanin ‘Yar Jami’ar da ta Shiga Muhimmin Kwamitin da Tinubu ya kafa

Kamfanonin siminti na Dangote da BUA sun koka kan tsadar fetur

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanonin su ka fitar na rabin shekara, inda su ka bayyana hakan da cire tallafin man fetur da kuma faduwar dajarar Naira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamfanonin har ila yau, sun samu tasgaro a harkokinsu musamman yadda kayan masarufi su ka kara tashi da kashi 22.41.

Rahotanni sun tabbatar cewa harajin da su ke bayarwa ya kai Naira biliyan 242.219 idan aka kwatanta da na 2022 kan Naira biliyan 233.467.

Nawa kamfanonin siminti na Dangote da BUA su ka kashe?

Nairametrics ta tattaro cewa kamfanin siminti na Dangote ya kashe Naira biliyan 157.020 kan siyan man fetur a cikin watanni shida idan aka kwatanta da Naira biliyan 129.957 a shekarar 2022 da karin kashi 20.82.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Ribar kamfanin bayan haraji ya tashi daga Naira biliyan 178.603 a cikin watanni shida idan aka kwatanta da Naira biliyan 172.104 a 2022.

Kamfanin siminti na BUA ya kashe Naira biliyan 47.907 kan fetur a watanni shida na wannan shekara, yayin da ya samu ribar Naira biliyan 63.616 idan aka kwatanta da Naira biliyan 61.363 na 2022.

Yadda Dangote Ya Bani Shawarar Neman Gwamna Da Kuma Daukar Nauyi Na, Gwamna Sule

A wani labarin, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana yadda Aliko Dangote ya dauki nauyin kamfen din siyasarsa gaba daya.

Sule ya ce Dangote ne ya ba shi shawarar tsayawa takara tun farko inda ya bayyana irin taimakon da attajirin ya masa a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel