Atiku Abubakar Na Ba da Tallafin N100,000? An Bankado Shirin Wasu Mazambata

Atiku Abubakar Na Ba da Tallafin N100,000? An Bankado Shirin Wasu Mazambata

  • Rahotanni sun bayyana cewa, akwai wasu shafuka a dandalin Facebook wadanda ke ikirarin cewa Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000
  • Sai dai wani bincike da aka gudanar kan wannan ikirarin, ya bankado yadda masu wallafar ke amfani da hoton Abubakar domin damfarar mutane
  • Rahoton bincike ya nuna cewa, Abubakar ko hadimansa ba su sanar da ba da wannan tallafi ba, karya ce kawai aka shirya da nufin yaudarar mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata sanarwa da aka wallafa a Facebook ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar yana raba wa 'yan Najeriya kyautar naira 100,000 kwatankwacin dalar Amurka 66.

Sanarwar ta ce: “Kyautar naira 100,000 don tallafa muku. 'Yan Najeriya, Ina tare da ku a koda yaushe. (Danna likau din kasa don neman tallafin)."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ainihin abin da ya jawo karancin abinci da tsadar rayuwa

Atiku Abubakar, dan takarar PDP
Atiku Abubakar bai fara rabon naira 100,000, aikin 'yan damfara ne. Hoto: Africacheck.org
Asali: UGC

An yi amfani da hoton Atiku don yaudara

Abubakar na jam'iyyar PDP ya zo na biyu a zaben shugaban kasar Najeriya a watan Fabrairun 2023, ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Africa Check ta gano cewa sanarwar na dauke da hoton jan hankali hade da hoto Abubakar, wanda idan ka taba shi zai kai ka zuwa shafin da ake tsammanin yin rajistar samun kudin.

An sake wallafa wannan tallan a wurare daban-daban a Facebook kamar a nan da kuma nan shafin.

Hattara da 'yan damfara a yanar gizo

Amma Abubakar yana rabawa ‘yan Najeriya naira 100,000, kuma yana yin hakan ta hanyar sanarwar ta bayar?

Latsa wa kan likau din da ke jikin sanarwar zai kai mu zuwa ga wani shafin yanar gizo da ke tallar damarmakin samun aiki da biza kyauta zuwa Amurka.

Kara karanta wannan

"Ku dauke kudinku": Binance ya dakatar da hada-hadar Naira, ya aika sako ga 'yan Najeriya

Wannan misali ne na aikin 'yan damfara, wadanda ke wallafa labarin karya mai jan hankali don jan ra'ayin mutane su je zuwa ga wani shafi da suke jagoranta.

Atiku ko makusantansa ba su sanar ba

Har ila yau, ba a rubuta sakon da kyau ba, yana dauke da kalmomin da ba a rubuta su daidai ba, sabanin yadda Abubakar ko hadimansa ke rubutu bisa ka'ida.

Mun duba shafin Abubakar na X (tsohon Twitter) amma ba mu samu labarin yana bayar da kyautar naira 100,000 ga ’yan Najeriya ba.

Babu wata majiya mai tushe ta kafafen yada labarai da ta bayar da rahoton irin wannan tallafin kudin, wanda hakan ya dada sanya mana shakku kan wallafar.

Gwamnati ta kaddamar da shirin tallafin kudi

A wani labarin, gwamnatin tarayya, ta kaddamar da shirin tallafawa akalla 'yan Najeriya miliyan 62 don rage masu radadin janye tallafin man fetur.

Gwamnatin ta kaddamar da wannan shiri ne Abuja, inda ta sanar da cewa kowanne mutum zai samu tallafin naira 25,000 har na tsawon wata hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel