An Shiga Tashin Hankali da Fursuna Ya Karbe Bindigar Jami'i, Ya Harbe Wani Mutum

An Shiga Tashin Hankali da Fursuna Ya Karbe Bindigar Jami'i, Ya Harbe Wani Mutum

  • Al'ummar da ke zaune a yankin gidan yarin Oke-Kura, birnin Ilorin, jihar Kwara, sun shiga tashin hankali a safiyar ranar Juma'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa wani fursuna ya kwace bindigar ganduroba tare da harbe wani bakanike da ke tsaye a gefen titi
  • Fursunan kamar yadda aka ruwaito, ya kwakwace bindigar ganduroban ne a lokacin da ake kokarin fitar da su daga gidan yarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ilorin, jihar Kwara - Wani fursuna a gidan yarin Oke-Kura a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya harbe wani bakanike da ke tsaye a gefen hanya bayan kwace bindigar ganduroba.

Motar jami'an hukumar gidajen yari.
Fursuna ya kwace bindigar ganduroba a Ilorin, jihar Kwara. Hoto: Sodiq Adelakun/Channels TV
Asali: UGC

Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da gandurobobi ke kokarin fitar da wasu fursunoni daga gidan yarin.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

A lokacin ne daya daga cikin fursunonin ya kwace bindigar wani ganduroba ya yi harbe-harbe inda harsashi ya samu bakaniken da ke a gefen titi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hankalin mazauna yankin ya tashi

Rahoton Daily Post ya nuna cewa tuni aka garzaya da bakaniken da aka harba a ciki zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa.

Yayin da shi kuma fursunan da ya yi harbin aka tsare shi a ofishin ‘yan sanda na ‘C’ Division da ke Isale-Ojo, a cikin babban birnin Ilorin.

Lamarin dai ya faru da misalin karfe 8:00 na safe, kuma ya haifar da firgici ga mazauna yankin wadanda suka ranta a na kare domin tsira da rayuwarsu yayin harbe-harben.

An cafke fursunan da ya tsere a Katsina

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun kamo wani fursuna da ya tsere daga gidan gyaran hali na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar NSCDC ta kama dattijo mai shekaru 85 da laifin garkuwa da karamin yaro

Hukumar kula da gidajen yari ta jihar Katsina, ta baki kakakinta, ASC Najibullah Idris, ta bayyana cewa jami'an tsaron sun kama fursunan a jihar Kaduna bayan bin diddiginsa.

A watan Oktobar shekarar da ta gabata ne fursunan tare da wani abokinsa suka tsere daga gidan yarin, inda aka fara kama abokin, daga bisani kuma aka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel