"Za Mu Dauki Mataki": Ministan Tinubu Ya Gayyaci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki

"Za Mu Dauki Mataki": Ministan Tinubu Ya Gayyaci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki

  • Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Bola Tinubu ta ja kunnen kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya
  • Hakan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi kan rashin wadatacciyar wutar lantarki da ake fama da ita a ƙasar nan
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, a ranar Laraba, ya bayyana cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC) za su fuskanci hukunci idan suka kasa yin aikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Biyo bayan rashin samun wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, ministan makamashi, Bayo Adelabu, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, ya yi barazanar soke lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki saboda rashin yin aikinsu.

Kara karanta wannan

Rayuka da dama sun salwanta yayin da aka samu barkewar rikici, bidiyo ya fito

A wani dogon rubutu da ya yi a shafinsa na X ranar Laraba, Adelabu ya koka kan rashin wadatacciyar wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.

Adelabu ya gargadi Discos
Adelabu ya yi barazanar soke lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki Hoto: Adebayo Adelabu, Prime Business Africa
Asali: Facebook

Adelabu ya bayyana cewa, duk da ƙoƙarin da ake yi na inganta lamarin, wutar lantarki na ci gaba da raguwa a ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya danganta matsalar rashin samar da wutar lantarki a Najeriya da rashin aikin da wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki ke yi da ɓarnata kayayyakin wutar lantarki a Abuja, Benin, Fatakwal da Ibadan.

Wane mataki ministan ya ɗauka?

Domin shawo kan lamarin, Adelabu ya ce ya kira shugabannin kamfanonin AEDC, IBEDC, da kuma manajan darakta na kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro.

Ya ƙara da cewa taron na da nufin tattaunawa kan tabarbarewar wutar lantarki a yankunansu tare da samar da mafita mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Zaman majalisa ya samu cikas yayin da aka shiga duhu, bidiyo ya bayyana

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"A matsayina na ministan makamashi na damu matuƙa game da tabarbarewar wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, a kan wannan batu, na gayyaci shugabannin kamfanonin rarraba wutar lantarki na AEDC, IBEDC da manajan daraktan kamfanin TCN zuwa wani muhimmin taro.
"Maƙasudin wannan taro shi ne tattauna tabarbarewar wutar lantarki a yankunansu tare da samar da mafita mai ɗorewa.
"Abin takaici ne ganin yadda wutar lantarkin ta ragu, duk da kokarin da ake yi na inganta lamarin."

- Bayo Adelabu

Za a daina ɗauke wuta a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya fara yunƙurin ganin an samu wadatacciyar wutar lantarki ta sa'o'i 24 a lokacin azumin Ramadan.

Gwamnan ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin ganin al'ummar jihar sun yi azumi cikin walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel