Minista Ya Dauki Zafi, Ya Kama Shirin Daukar Matakin Matsalar Wutar Lantarki

Minista Ya Dauki Zafi, Ya Kama Shirin Daukar Matakin Matsalar Wutar Lantarki

  • Ministan makamashi bai jin dadin yadda ake fama da karancin wutan lantarki a wasu garuruwan Najeriya a wannan lokaci
  • Adebayo Adelabu ya kira shugabannin kamfanonin da ke raba wutar lantarki domin jin inda ake samun matsalar lantarkin
  • Mai magana da yawun Adelabu, ya fitar da jawabi a ranar Asabar cewa Minista zai zauna da shugaban kamfanin TCN na kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya aika sammaci ga wasu shugabannin kamfanonin lantarki da ke kasar nan.

Mai girma Ministan ya dauki wannan mataki ne a dalilin irin tabarbarewar rashin lantarki a yankunan da kamfanonin nan suke aiki.

Wutar Lantarki
Minista zai ji menen matsalar wutar lantarki Hoto: NERC, LightHouse
Asali: UGC

Ministan lantarki ya yi jawabi

The Guardian ta ce Bolaji Tunji ya fitar da jawabi na musamman a madadin Minista, ya shaida matakin da mai gidansa ya dauka a yau.

Kara karanta wannan

Buhun siminti zai yi arha, Shugaba Tinubu ya aike da saƙon farashi ga Dangote, BUA da wasu kamfanoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Tunji shi ne mai magana da yawun bakin Adebayo Adelabu wanda aka nada a matsayin Minista bayan kin karbar Nasir El-Rufai.

Mai magana da yawun bakin Ministan ya ce an gayyaci shugabannin da ke rike da kamfanonin AEDC da IBDEC domin a ji ta bakinsu.

Latntarki: Za a zauna da DisCos da TCN

Bayan haka, Punch ta ce an aika sammaci ga shugaban TCN, Sule Ahmed Abdulaziz.

Shugabannin kamfanonin nan da ke raba wuta a kewayen birnin Abuja da garin Ibadan za suyi bayanin matsalolin da ake samu.

Ana sa rai a wajen wannan zama da za a yi, a fito da mafita a kan sha’anin lantarkin da ake ta alkawarin za a inganta shi a kasar.

Wanene da laifi a matsalar lantarki?

The Cable ta ce ana zargin cewa kamfanonin raba wuta ba su karbar wutan da ake samu daga kamfanin TCN mai alhakin aika lantarkin.

Kara karanta wannan

Yadda aka damke shugabannin kamfanin Binance daga kasar waje a yunkurin karya Dala

Bayan haka Ministan yana zargin miyagu sun lalata layin wuta wasu garuruwa da suka hada Benin, Fatawal da ita kan ta birnin tarayya.

Daga nan kuma Adelabu zai zauna da sauran kamfanonin DisCos a shirin ladabtar da su, ko abin ya kai gwamnati ta karbe lasisin na su.

'Dan APC ya tabo gwamnatin Tinubu

A babin siyasa, an ji labari Salihu Mohammed Lukman ya na ganin gwamnatinsu ta APC tana dauko shawarwarin turawan yamma.

Jagora a APC ya ce bayan an sha wahala wajen kafa jam’iyya a 2013, shugabanni sun yaudari talaka, an koma aiki da dabarun IMF.

Lukman ya ce Tinubu yana tafiyar da gwamnatinsa kamar soja kuma ba a damawa da kowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel