Bututun Mai Ya Kama Da Wuta A Rivers, Ya Hallaka Gomman Barayin Danyen Mai

Bututun Mai Ya Kama Da Wuta A Rivers, Ya Hallaka Gomman Barayin Danyen Mai

  • Wasu mutane sun gamu da ajalinsu cikin dare yayinda suke diban danyen man fetur a jihar Rivers
  • Fashe-fashen bututun mai a yankin Neja Delta na daya daga cikin abubuwan da gwamnati ke kuka kai
  • Gwamnatin tarayya ta dauki Government Tompolo aikin gadin bututun man gwamnati a yankin

Ana fargabar gomman mutane sun mutu sakamakon tashin gobara a gindin satar danyen mai daga bututun man gwamnati a unguwar Rumuekpe, karamar hukumar Emohua ta jihar Rivers.

Wadanda aka ruwaito sun hallaka ana zargin masu fasa bututun mai ne suna satar danyen mai suna tacewa.

Diraktan cibiyar wayar da kan matasa da yanayi, Fyneface Fyneface, ya tabbatar da hakan a jawabin da cibiyar tayi ta shafin COSAS, rahoton TheNation.

Butuntun mai
Bututun Mai Ya Kama Da Wuta A Rivers, Ya Hallaka Gomman Barayin Danyen Mai
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

Fyneface yace gobarar ta auku ne misalin karfe 2 na daren Juma'a yayinda wani direban ya tayar da daya daga cikin motocin da ake amfani wajen satar danyen man.

Ana amfani da motar ne wajen tafiyar da man sata zuwa cibiyoyin tace danyen mai na bayan fagge.

Gobarar da ta auku a bututun man Trans-Niger Delta Pipeline (TNP), ta haddasa mutuwar mutane da dama a unguwar ciki har da mata, TheNation ta ruwaito.

Hakazalika motoci da babura da dama sun kone kurmus.

An tattaro cewa mutanen da ke wajen, masu diban man da masu lodi cikin mota ne suka mutu gaba daya.

An tura sojoji da yan sanda wajen, rahoton ya kara.

Kowa zai samu: NNPC yayi Alkawarin yana da litan fetur bilyan 2 a ajiye

A wani labarin kuwa, kamfanin arzikin man Najeriya NNPC ya bayyana cewa yana da isasshen man fetur na lita 1.805 biliyan wanda zai ishe kowa nan da kwanaki 30.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Majalisar Jihar Kogi Ya Rasu Bayan Zabe

Kamfanin da kansa ya bayyana hakan a hoton bayanin da ya daura a shafinsa na Facebook.

Hakazalika Kakakin NNPCL, Garbadeen Muhammad, ya bayyana hakan ranar Litinin, 20 ga Febrairu a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Ya yi bayanin cewa yanzu haka akwai litan mai miliyan 803.35 a depot yayinda akwai lita bilyan 1 kan jirgin ruwa.

Ya kara da cewa kamfanin ya tanadi yadda za'a samu isasshen man fetur daga yanzu har zuwa karshen watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel