Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Matasa Marasa Aikin Yi Alawus, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Matasa Marasa Aikin Yi Alawus, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, matasa za su dara bayan alkawarin da Tinubu ya yi musu kan tallafi
  • Matasan da za su ci gajiyar shirin sun hada da wadanda ba su da aiki masu ɗauke da kwalin digiri ko na kwalejin ilimi
  • Hausa Legit ta ji ta bakin wasu matasa da suka kammala karatu babu aikin yi a Gombe inda bayyana ra'ayoyinsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan m da ba su da aikin yi alawus duk wata a Najeriya.

Shirin zai taimakawa matasan ne da ke da kwalin digiri ko na kwalejin ilimi don tsame su daga kunci.

Kara karanta wannan

A fadi illar da Kiripto ke yi wa tattalin arziki yayin da aka cafke shugabannin Binance, za a haramta

Matasa za su fara karbar alawus don rage musu radadin halin da ake ciki
Matasa za su caba yayin da Gwamnatin Tarayya za ta fara ba su alawus. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Menene dalilin ba da tallafin ga matasa?

Ministan kudade a Najeriya, Wale Edun shi ya bayyana haka a jiya Litinin 26 ga watan Faburairu a Abuja., Cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"A wannan yanayi da ake ciki na tsadar kaya, mai girma shugaba kasa ya himmatu wurin taimakon marasa ƙarfi don samun damar siyan kayan.
"Ya umarci samar da hukuma wacce za ta kula da matasan da ba su da aikin da kuma sauran al'umma.
"Nan ba da jimawa ba, za mu samar da tsarin tallafawa matasa da ba su da aiki."

Edun har ila yau, ya ce shugaban ya bukaci a yi gaggawar samar da hanyar dakile wahalalun da ake sha a kasar.

Sauran tsare-tsaren da za su rage radadi

Ministan ya ce shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila shi zai jagoranci kwamitin, cewar Western Post.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a cikin awa daya, Sheikh Daurawa

Hausa Legit ta ji ta bakin wasu matasa da suka kammala karatu babu aikin yi a Gombe kan lamarin.

Usman Abubakar Umar wanda ke harkar kasuwanci ya ce tabbas hakan zai taimaka musamman idan aka bi tsarin N-Power.

Ya ce:

"Kamar yadda aka bi tsarin N-Power idan har za a bi tsarin da ya dace tabbas hakan zai ragewa matasa marasa aikin yi radadi.

Auwal Ahmed wanda malamin makaranta ne ya ce:

"Muna fatan samun cin gajiyar wannan shiri saboda a gwamnatin baya an yi tsare-tsare masu kyau.
"Sai dai matsalar da na ke tsoron za ta iya faruwa shi ne bai wa wadanda basu dace da kuma barin wadanda suka dace."

Tinubu ya amince da rahoton Oronsaye

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da rahoton Stephen Oronsaye don yin amfani da shi.

Tinubu ya umarci amfani da rahoton ne don dakile yawan kashe kudaden da gwamnati ke yi ganin yadda hukumomi suka yi yawa.

Rahoton dai ya na dauke da wasu tsare-tsare ne da za su rusa wasu hukumomi da kuma hade wasu wuri guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel