
ASUU







Kungiyar ASUU tace dole a biya ta albashin watannin nan takwas a lokacin yajin-aiki. Idan ba a sasanta ba, Iyaye da Dalibai za su ji jiki a sabon rikicin na su.

Ministan ilimi, Malam Adamu a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba ya bayyana matsayin gwamnatin tarayya cewa ba zata biya malaman ASUU kudin aikin da basu yi ba.

'Yan ASUU za su ki koyar da dalibai karatu a duka jami’o’in gwamnati. Malaman Jami’a sun tsaida matakan da za a dauka bayan biyansu rabin albashi a watan Oktoba

Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya bayyana cewa shi tare da takwarorinsa 35 na jihohin Najeriya suna iyakar kokarinsu wurin sasanci tsakanin ASUU da FG.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta raba albashin malaman jami'a biyu don biyan malaman jami'a da suke bin bashin watanni takwas yanzu.

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ta biya albashin kwana 18. ASUU tace su malamai ne ba ma’aikatan wucin-gadi ba.
ASUU
Samu kari