Tsadar Rayuwa: An Caccaki NLC Kan Dakatar da Zanga-Zanga, An Fadi Kuskuren da Ta Yi

Tsadar Rayuwa: An Caccaki NLC Kan Dakatar da Zanga-Zanga, An Fadi Kuskuren da Ta Yi

  • Deji Adeyanju ya yi Allah wadai da matakin da NLC ta ɗauka na dakatar da zanga-zangar da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi a faɗin ƙasar nan
  • Adeyanju wanda mazaunin Abuja ne ya yi nuni da cewa ƴan Najeriya da dama ba su aminta da ƙungiyar da Joe Ajaero ke jagoranta ba
  • A daren ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, ƙungiyar NLC ta dakatar da zanga-zangar ta kwanaki biyu tare da ƙara wa gwamnatin tarayya wa’adi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Deji Adeyanju, wanda tsohon ɗan jam’iyyar PDP ne ya caccaki ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kan dakatar da zanga-zangar da take yi bayan kwana ɗaya kacal.

Legit Hausa ta rahoto cewa NLC ta shaidawa ƴan Najeriya cewa za ta fara zanga-zanga ta kwanaki biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Wata mata ta shiga gagarumar matsala bayan ta ci zarafin jami'ar 'yar sanda a Legas

An caccaki kungiyar NLC
Bayan kwana daya NLC ta dakatar da zanga-zanga Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Sai dai a daren ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, shugabancin ƙungiyar ta NLC, ta umurci mambobinta da su dakatar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar NLC, zanga-zangar da aka yi a safiyar Talata, 27 ga watan Fabrairu ta samu gagarumar nasara.

Da yake mayar da martani game da hakan, Adeyanju ya soki ƙungiyar NLC, yana mai cewa "babu sauran wanda ke ganin ƙimarsu a Najeriya"

Ya rubuta hakan ne dai a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a daren ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu.

A kalamansa:

"Babu wani abu da aka cimma daga zanga-zangar yau amma NLC ta dakatar da yajin aikin. NLC, ina fatan kun ga dalilin da ya sa babu wanda ke ganin ƙimar ku a Najeriya!"

Wane martani ƴan Najeriya suka yi?

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta yi kamu mafi girma a tarihinta, bayanai sun fito

Da alama wasu ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yarda da kalaman Adeyanju.

Legit Huasa ta ɗauko wasu daga cikin martanin da aka yi. Ga su nan a ƙasa:

@christianofans4 ya rubuta:

"Dala ta shiga aljihu."

@real_ndubuisi ya rubuta:

"Akwai wani karin maganar Igbo da ke cewa: “Ogbu mma Tabaka ka ewere mma ga ya n’azụ.” Bayan ƴan adawa (APC a yanzu) sun yi amfani da ƙungiyar NLC wajen gurgunta gwamnatin Jonathan, sun tabbatar sun ruguza ta. A gare ni, duk wata NLC ko TUC sun daina wanzuwa bayan zanga-zangar tallafin man fetur na Janairun 2012."

@Adesanyajnr ya rubuta:

"Ban san dalilin da yasa har yanzu mutane ke ɗaukar wannan NLC da muhimmanci ba, NLC ta ƙarshe ta ƙare da Oshiomole."

Gwamna Makinde Ya Shiga Zanga-Zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya shiga zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ke yi kan tsadar rayuwa.

Gwamnan a yayin da yake jawabi a wajen zanga-zangar ya tabbatar da cewa lallai ana fama da yunwa a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel