“Dino Ya Tsallake”: Tsohon Sanatan PDP Ya Saki Satifiket Din Tsira Daga Hannun Tinubu

“Dino Ya Tsallake”: Tsohon Sanatan PDP Ya Saki Satifiket Din Tsira Daga Hannun Tinubu

  • Tsohon ‘dan takarar gwamnan PDP a Kogi, Dino Melaye, ya yada wani satifiket na tsira daga hannun Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Jigon na PDP ya yi hannunka mai sanda game da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki, wanda ya yi sanadiyar gudanar da zanga-zanga a jihohin kasar
  • ‘Yan Najeriya da dama sun garzaya sashin sharhi domin bayyana ra’ayoyinsu game da tsohon sanatan na Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Dino Melaye, tsohon sanatan jam’iyyar PDP, ya saki wani satifiket na tsira daga hannun Shugaba Bola Tinubu, wanda shagube ne ga halin da ake ciki na tsadar rayuwa a kasar.

A baya-bayan nan ne aka gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, haka kuma mambobin kungiyar kwadago ta kasa ma sun yi irin haka saboda tsadar kayan abinci.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Dino ya yi shagube ga Tinubu
“Dino Ya Tsallake”: Tsohon Sanatan PDP Ya Saki Satifiket Din Tsira Daga Hannun Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Dino Melaye
Asali: Twitter

An yi zanga-zangar ne kan cire tallafin man fetur, wanda shine ya haddasa matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ‘yan Najeriya ke cewa game da Melaye da Tinubu

Da yake martani kan halin da kasar ke ciki, Melaye, wanda ya kasance ‘dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi da aka yi a baya-bayan nan, ya garzaya shafin X don wallafa satifiket dinsa na tsira daga Tinubu.

‘Yan Najeriya da dama sun garzaya sashin sharhi na wallafar da ya yi don bayyana ra’ayoyinsu.

Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

Eze ya yi martani:

"Dino ya tsallake. Ina tayaka murna yallabai.”

Goldman Steve ya ce:

"Kawu, wai baka cikin matsalar ne? Ka manta rawar ganin da ka taka a 2015? Ka manta yadda Yahaya Bello ya zama gwamna a jihar Kogi? Babu abin da kake ji."

Kara karanta wannan

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin tarayya saboda abu 1, bidiyo ya bayyana

Jerry Govilla ya ce:

"A matsayin sanata, wani amfani ka yi wa mutanenka? Ba wai samun kudi bane iya kula da kudin ne. Babu abin da za ka ce ko ka yi da zai yi tasiri wajen 'yan Najeriya, don haka ka huta."

Ga wallafarsa a kasa:

An caccaki NLC kan dakatar da zanga-zanga

A wani labarin, mun ji cewa Deji Adeyanju, wanda tsohon ɗan jam’iyyar PDP ne ya caccaki ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kan dakatar da zanga-zangar da take yi bayan kwana ɗaya kacal.

Legit Hausa ta rahoto cewa NLC ta shaidawa ƴan Najeriya cewa za ta fara zanga-zanga ta kwanaki biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel