Ministar Tinubu Ta Fadi Mataki 1 da Ya Kamata Mata Su Dauka Yayin Cacar Baki da Mazajensu

Ministar Tinubu Ta Fadi Mataki 1 da Ya Kamata Mata Su Dauka Yayin Cacar Baki da Mazajensu

  • Ministar Shugaban kasa Bola Tinubu ta aika sako mai muhimmanci ga matan da ke so aurensu ya yi karko har mutu-ka-raba a Najeriya
  • Uju Kennedy-Ohaneye, ministar harkokin mata, ta bukaci mata da kada su dunga cacar baki ko fadan jiki da mazajensu a gida
  • Ministar ta yi wadannan kalamai masu cike da hikima ne a yayin taron kwamishinonin ma’aikatun mata na jihohi a ranar Laraba a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, ta shawarci mata a kasar da su daina yin sa'insa ko fada da mazajensu yayin da sabani ya gibta tsakaninsu a gida.

Ministar mata ta ba matan Najeriya shawara mai amfani
Ministar Tinubu Ta Fadi Mataki 1 da Ya Kamata Mata Su Dauka Yayin Cacar Baki da Mazajensu Hoto: Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

Ministar ta bayar da shawarar ne a yayin wani taron kwamishinonin ma’aikatun mata na jihohi a Najeriya, wanda aka yi a ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Matar aure ta nemi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda dalili 1 tak

Ministar Tinubu ta ba mata shawara

Kennedy-Ohaneye ta ce guje wa cacar baki zai hana cin zarafi da ka iya kai ga jin rauni ko mutuwa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tori News ta nakalto ministar na cewa:

"Ina kuma rokon mata akan kada su tsokano rigima, koda kuwa a gida ne. Ku zauna lafiya a gidanjenku saboda idan akwai zaman lafiya a gida, toh macen ciki ce ta bayar da gudunmawar kaso 80 cikin dari a ciki.
"Idan kina bukatar zaman lafiya, toh za ki iya cimma hakan. Ki yi shiru da bakin ki.
"Mayar da martani ba zai haifar da 'ya'ya masu idanu ba, maimakon haka zai kai ga mutuwa ko barna, yana haifar da tayar da yara marasa tarbiya cikin al'umma.
"Ki yi shiru da bakinki, ba yana nufin baki da wayo bane illa dai ki zama mace mai hikima. Idan namiji yana ihu tare da fadin maganganu, yi kamar mara wayo sannan ki yi shiru da bakinki.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

"Bayan wani 'dan lokaci, ki sa idon kansa. Idan har namijin kirki ne, zai dawo ya ba ki hakuri. Idan ba na kirki bane, share shi. Ki ajiye abin da kike son yi a zuciyarki, amma idan muka nuna mun isa sannan muka rama, yawancin lokuta, yana kai ga duka, ana iya ji maki rauni"

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wasu matan aure kan wannan shawara da ministarsu ta bayar.

Fatima Ibrahim ta ce:

"Gaskiya ministar mata ta bayar da muhimmiyar shawara wanda duk macen da ta yi amfani da ita za ta ga haske a gidan aurenta. Yawanci idan ka duba musababbin mace-macen aure musamman ma mu a nan Arewa duk rashin hakuri ke kawo shi.
"Mazanmu akwai su da tsare gida, toh da zaran sun yi magana aka mayar masu gani suke mace bata da tarbiya, sai ka ga abu karami ya zama babba.

Zainab Abdullahi kuwa cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

"Lallai wannan shawara ce mai kyau da ya kamata matan aure su dauka. Babu abin da ya kai sa'in'sa kawo tangarda a zamantakewar aure. Amma idan mace ta yi hakuri ta yi sanyi a lokacin da miji ya dau zafi sai ka ga magana ta mutu tun ba'a kai ko'ina ba."

Likita ya wayar da kan ma'aurata kan kwanciyar aure

A wani labarin kuma, mun ji cewa Eric Okunna, wani kwararren likitan mata, ya yi jawabi kan alfanun da ke tattare da kwanciyar aure mai nagarta tsakanin mata da maza.

Likitan ya nemi jin ta bakin wasu al'ummar Anambra, kan batutuwan da suka shafi rayuwar ma'aurata musamman kwanciyar aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel