Lafiya jari: Hanyoyi 5 da za ku kula da kan ku cikin lokacin hunturun sanyi
Lokacin sanyi musamman ma a kasar Hausa kan zo da wani nauyi na yanayin busasshen iska da kura. Haka zalika ma dai yanayin kan auku ne a tsakanin watannin Nuwambar kowace shekara da kuma watan Maris na shekarar gaba a kirgan kwanan watan bature.
A lokacin sanyi, akwai cututtuka da dama da kan addabi al'umma don haka ma Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin hanyoyin da za ku kare kanku:
KU KARANTA: Gwamnan Ebonyi ya bukaci Buhari ya tsaya takara
1. Sanya kayan sanyi masu nauyi nada matukar muhimmanci a wannan lokacin musamman ma ga yara da kuma tsofaffi domin kare kai.
2. Yana da matukar anfani, mutane su rika saka tubarau da zai rika rufe masu idanuwansu da ma hanci da baki a wasu lokuta domin samun kariya.
3. Yana da kyau mutane su rika shafa mai da ke da maiko sosai a wannan lokacin domin samun laushin fata musamman ma a baki da kuma kafa.
4. Yana da kyau a rika wanke kayan abinci da ganyayyaki da ma 'ya'yan itatuwa sosai kafin ci a wannan lokacin.
5. Haka zalika atisaye da motsa jiki yana da matukar anfani shima domin samun dumamar jiki da kuzari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng