Fasaha: Kamfanin MTN ya shigo da sabuwar hanyar sadarwa ta 5G a nahiyyar Afirka
Kamfanin sadarwa na MTN ya shigo da sabuwar fasahar zamani ta 5G wadda ka iya baiwa ma'abotanta damar shiga tare da yin debe-debensu a yanar gizo cikin kiftawar idanu.
Wannan itace mafi kololuwar nasara a kan hanyar sadarwar wayar salula a Afrika kamar yadda kamfanin na MTN ya bayyana a sanarwar ranar Litinin din da ta gabata.
Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Trust cewa, wannan sabuwar fasahar ta zamani da kamfanin ya shigo da ita zai baiwa ma'abota shiga yanar gizo wata manhaja ta saukakawa da babu makamanciyar a duk nahiyyar Afirka.
KARANTA KUMA: Akwai bukatar Buhari ya rairaye masu yiwa gwamnatin sa zagon kasa - Chukwuani
Shugaban kamfanin reshen kasar Afirka ta Kudu, Giovanni Chiarelli ya bayyana cewa, babu shakka wannan sabuwar fasahar sadarwar ta 5G za ta baiwa mabukata damar shiga yanar gizo cikin kiftawar idanu ba tare da wani tsaiko ko jinkiri ba, sai dai akwai bukatar bakan gizo mai yalwa domin cimma manufar.
A halin yanzu, kamfanin sadarwa na MTN yana da lasisin fasahar sadarwa ta 4G a Najeriya wadda yake neman hanyar bunkasa ta da fasahar 5G a lokuta mafi kusa na nan gaba.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng