"Akwai Yunwa a Kasar: Gwamnan PDP Ya Shiga Zanga-Zangar ‘Yan Kwadago a Jiharsa

"Akwai Yunwa a Kasar: Gwamnan PDP Ya Shiga Zanga-Zangar ‘Yan Kwadago a Jiharsa

  • Gwamna Seyi Makinde ya shiga cikin 'yan kwadago da suka gudanar da zanga-zanga a Ibadan a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar
  • Makinde ya bayyana cewa, tabarbarewar tattalin arzikin ba na jihar Oyo kadai ba ce, illa dai batu ne na kasa baki daya
  • Gwamnan na Oyo ya ce yana sane da wahalhalun da mutane ke sha, yana mai alkawarin cewa zai kasance cikin wadanda za su kawo gyara a kasar nan

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Ibadan, jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shiga cikin 'yan kwadago da suka gudanar da zanga-zanga a garin Ibadan, a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, a wajen zanga-zangar, Gwamna Makinde ya yarda cewa ana fama da yunwa a kasar.

Gwamnan Oyo ya shiga zanga-zangar Oyo
"Akwai Yunwa a Kasar: Gwamnan PDP Ya Shiga Zanga-Zangar ‘Yan Kwadago a Jiharsa Hoto: @Daveman
Asali: Twitter

A cewar gwamnan na Oyo, wahalar da ake sha a kasar ya kai kololuwa, inda mutane da dama basa iya ciyar da kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, Makinde ya yi kira da kwantar da hankali da fahimtar juna. Ya kuma bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta dauki mataki don kawar da wahalar da mutane ke sha.

Jaridar Leadership ta nakalto Makinde yana cewa:

"Akwai yunwa da wahala a kasar nan. Dole mu yi wani abu a kai."

A halin da ake ciki, rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta shiga aikin sintiri a fadin kananan hukumomi 33 na jihar. An yi hakan ne domin hana karya doka da oda yayin zanga-zangar NLC.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta dakatar da sayar da kayan abinci kan farashi mai rahusa, ta faɗi dalili 1 tak

Jaridar Legit ta rahoto cewa zanga-zangar da ke gudana ya biyo bayan cikar wa'adin kwanaki 14 da aka bai wa gwamnatin tarayya ne don aiwatar da matakanta kan wahalar da ake sha.

Kungiyar kwadago ta yi tattaki a majalisar dokoki

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Joe Ajaero ya jagoranci dubban masu zanga-zanga zuwa majalisar dokokin tarayya, domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwa a kasar.

An gano jami'an hukumomin tsaro daban-daban girke a hanyoyin shiga da fita daga majalisar, musamman ma a bangaren sakatariyar tarayya domin kula da yadda ake tafiyar da zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel