Amarya Ta Sharbi Kuka da Hawaye Ranar Bikinta Saboda Wani Babban Al’amari 1, Bidiyon Ya Yadu

Amarya Ta Sharbi Kuka da Hawaye Ranar Bikinta Saboda Wani Babban Al’amari 1, Bidiyon Ya Yadu

  • An gano wata amarya da ta cika da bakin ciki tana sharbar kuka babu kakkautawa a wani bidiyo da ya yadu saboda mai daukar hotonta ya ki zuwa
  • An rahoto cewa musamman amaryar ta dauki mai hoton, amma ko sama ko kasa ba a gan shi ba a ranar bikin
  • Mutane da dama da suka ga yadda amaryar ke kuka sun ce irin haka ya taba faruwa da su a baya inda aka ba su kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata amarya ta cika da bakin ciki saboda mai daukar hoton da ta dauko ya ki hallara domin daukar su hotuna a rana mafi girma da muhimmanci a gareta.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano 'yan uwa da abokan arziki kewaye da amaryar yayin da take hawayen bakin ciki.

Kara karanta wannan

Matashi ya bugo keke daga jihar Benue don ziyartan Ahmed Musa a gidansa

Amarya ta yi kukan rashin zuwan mai hoto
Amarya Ta Sharbi Kuka da Hawaye Saboda Wani Babban Al’amari 1, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Instagram/@flawlessfacebytoria.
Asali: Instagram

@flawlessfacesbytoria ce ta wallafa bidiyon a Instagram, inda ta ce da gangan amaryar ta zabi wannan mai daukar hoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar labarin, amaryar ta yi kuka na tsawon awa daya yayin da 'yan uwa da kawayenta suka yi kokarin kwantar mata da hankali.

Sai dai kuma, mai hoton ya turo wani daban domin ya dauki hotunan bikin.

An yi wa bidiyon take da:

"Mai daukar hoton ya yanke shawarar kin zuwa sannan ya turo wani mai hoton na daban domin ya dauki hotuna ba tare da ya bayar da sanarwa kafin lokaci ba. Da gangan amaryar ta zabi wannan mai hoton domin ya dauki hotunan bikin."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

@chisom_soma ta ce:

"Abu makamancin wannan ya faru da ni da DJ na, kuma gayen da ya turo a matsayin wakilinsa ya bata mintuna 30 yana kokarin gano abin da ya faru da na'urar fitar da sautinsa."

Kara karanta wannan

Wata mata da ke siyar da gwanjo ta taki sa'a, ta tsinci daloli a kayan da ta bude

@adalene_jane ya ce:

"Wannan mummunan abu ne. Idan har ba a yi yarjejeniya a baya na kawo wani mai daukar hoton ba, zan yi karar mai hoton ne. Babu wani abu bayan wannan."

Budurwa ta yi kukan rasa saurayinta

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa a TikTok ta koka cewa sahibinta ya rabu da ita sannan ya auri wata daban bayan sun kwashe tsawon lokaci suna soyayya.

Ta bayyana a TikTok cewa mutumin ya karya mata zuciya bayan shekaru biyar suna soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel