Wata Mata Da ke Siyar da Gwanjo Ta Taki Sa’a, Ta Tsinci Daloli a Kayan da Ta Bude

Wata Mata Da ke Siyar da Gwanjo Ta Taki Sa’a, Ta Tsinci Daloli a Kayan da Ta Bude

  • Wata 'yar Najeriya ta taki sa'a bayan ta tsinci dala 200 a daya daga cikin kayan gwanjo da ta bude kwanan nan
  • Ta wallafa wani bidiyo a dandalin TikTok tana mai nunawa duniya dalolin cike da farin cikin wannan sa'a da ta taka
  • A yadda farashin dala yake a yanzu, dalar Amurka 200 daidai yake da N321,000, lamarin da yasa wasu suka ce ta ci riba biyu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata 'yar Najeriya da ke sana'ar gwanjo ta taki babban sa'a a daya daga cikin kayan da ta bude kwanan nan.

Ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda take fada ma mabiyanta cewa ta tsinci dala 200 a kayan gwanjon da ta siya.

Kara karanta wannan

Wani uba ya yi watsi da 'yan kai amarya, ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta da kansa, bidiyo

Matashiya ta tsinci daloli a gwanjo
Wata Mata Da ke Siyar da Gwanjo Ta Taki Sa’a, Ta Tsinci Daloli a Kayan da Ta Bude Hoto: TikTok/@jamfar_thrift
Asali: TikTok

An gano ta cikin murna a bidiyon tana mai baje kolin dala 200 da ta tsinta don mutane su gani yayin da take nuna farin cikinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun bayyanata a matsayin mai sa'a sosai saboda dala 200 a farashin canji a yanzu ya kai N321,000.

Wasu sun bayar da labarin yadda suma ko wasu nasu suka tsinci abu mai muhimmanci a cikin gwanjo.

Ta yi wa bidiyon take da:

"Kana iya siyan gwanjo ka ga kudi mai ma'ana a ciki."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da budurwa ta tsinci kudi a gwanjo

@swayjay ya ce:

"Na taba ganin dala 20 a wandon jeans na gwanjo."

@AnnieHairs Extension ta ce:

"Baabam makudan kudi kenan fa N320k da farashin dala a yanzu fa."

@Oo_Gee_Boss ta ce:

"Idan suka kawo maki kaya mara kyau kada ki yi kuka fa."

Kara karanta wannan

Hazikin matashi ya kera otal da katafaren gida daga kwalaye, bisararsa ta burge mutane

@Femi ya ce:

"Kawu na ya siya motar da aka yi amfani da ita kai tsaye daga USA sannan ya cimma zinare da ya kai naira miliyan 31 da wasu daloli."

Matashiya ta tsinci miliyan 1.5 a gwanjo

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wani ɗan Najeriya ya soki ƙanwar abokinsa da ke sayar da kayan sawa na gwanjo bayan ta yi wata tsintuwa.

Budurwar ta ci karo da wani abin mamaki inda ta tsinci dalar Amurka $1850 (N1.5m) da aka saka a cikin tarin kayan gwanjon da ta siya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel