Budurwa Ta Sharbi Kuka da Hawaye Yayin da Saurayinta Na Shekaru 5 Ya Yi Wuff da Wata

Budurwa Ta Sharbi Kuka da Hawaye Yayin da Saurayinta Na Shekaru 5 Ya Yi Wuff da Wata

  • Wata matashiyar budurwa ta shiga mawuyacin hali yayin da saurayin da take matukar so ya auri wata daban
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, matashiyar ta ce ita da saurayin sun shafe tsawon shekaru biyar suna tare kafin ya rabu da ita
  • Bidiyon ya nuno wasu jerin motoci wadanda ta yi hasashen cewa su ke dauke da amaryar da ta sace zuciyar sahibinta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar budurwa a TikTok ta koka cewa sahibinta ya rabu da ita sannan ya auri wata daban bayan sun kwashe tsawon lokaci suna soyayya.

Ta bayyana a TikTok cewa mutumin ya karya mata zuciya bayan shekaru biyar suna soyayya.

Budurwa ta koka bayan saurayinta ya auri wata daban
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: TiKTok/@ifunaya94 and Getty Images/Ekaterina Goncharova.
Asali: UGC

Bidiyon da ta wallafa a soshiyal midiya ya nuno ayarin motoci dauke da saurayin nata da kuma matar mijin a ranar aurensu.

Kara karanta wannan

"Zan iya zama ta 3 ko 4": Budurwa ta yi nutso a son Bello El-Rufai, tana so ya aureta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@ifunaya94 ce ta wallafa bidiyon, kuma ya haddasa martani da dama daga jama'a. Yayin da wasu mutane suka nuna shakku kan gaskiyarta, wasu sun tausaya mata.

Ya yi wa bidiyon take da:

"Saurayina ya je ya auri wata yarinya daban bayan ya shafe shekaru biyar yana soyayya da ni. Ba zan iya boye hawayena."

Jama'a sun yi martani

@mercyde7 ta tambaya:

"Kin tabbata ba ke bace amaryar a nan?"

@Globest ya yi martani:

"Nawoo ..ki yi amfani da juju ki lalata komai hajiya."

@rosejoseph918 ta ce:

"Wannan abu ne mai karya zuciya. Ya Allah kada ka sa wata bakuwa ta dauke matsayina."

@preciousnwaeze ta ce:

"Na san yadda kike ji yar'uwa, nawa bayan shekaru 7 ne."

@sugar ta ce:

"Nawa, mun shafe shekaru biyar muna soyayya amma ya ce ba zai aureni ba."

Kara karanta wannan

Wani uba ya yi watsi da 'yan kai amarya, ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta da kansa, bidiyo

Uba ya raka diyarsa dakin miji da kansa

A wani labarin, mun ji cewa kamar yadda aka saba bisa al'adar Mallam Bahaushe da mutanen Arewa, a duk lokacin da aka ce za a kai amarya dakin mijinta, 'yan uwa da abokan arziki kan taru su yi mata rakiya.

Mutanen Arewa tun zamanin baya suna mutunta wannan al'ada, inda a kauyukan karkara akan yi wa amarya rakiya ta hanyar yin wake-wake da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel