Yadda Amarya Ta Fashe Da Kuka a Wajen Biki Bayan Masu Abinci Sun Ki Bayyana, Bidiyon Ya Yadu

Yadda Amarya Ta Fashe Da Kuka a Wajen Biki Bayan Masu Abinci Sun Ki Bayyana, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata amarya ta fashe da kuka a ranar aurenta bayan masu abinci sun yi lattin isa wajen shagalin bikinta
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano amaryar zaune a kujera yayin da wani mutum ya dunga karfafa mata gwiwa ya kuma bata tabbacin yin bikin cikin nasara
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon, inda wasu da dama suka dunga mamakin dalilin jinkirin masu abincin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumi mai suna @blogwithmcb a TikTok ya wallafa wani bidiyo mai tsuma zuciya inda yake lallashin wata amarya a wajen shagalin bikinta.

A cewar mutumin mai karamci, amaryar ta karaya yayin da masu abinci da ya kamata ace sun isa wajen bikin tun karfe 2:00 na rana suka ki zuwa har karfe 4:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 25 Ta Siya Gida, Ita Ta Fara Mallakar Gida a Danginsu, Bidiyon Ya Tsuma Zukata

Amarya ta koka saboda rashin zuwa masu abinci a wajen bikinta
Yadda Amarya Ta Fashe Da Kuka a Wajen Biki Bayan Masu Abinci Sun Ki Bayyana, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @blogwithmcb/TikTok.
Asali: TikTok

Mahalarta biki sun karfafawa amaryar da ta shiga damuwa gwiwa

Ya ci gaba da karfafawa amaryar da ke zub da hawaye gwiwa, yana mai bata dalilai da za su sa ta farin ciki da fatan kammala taron bikin cikin nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"A wannan gabar, ta karaya saboda masu abincin da ya kamata su kasance a wajen bikin da karfe 2:00 na rana, sun ki hallara har zuwa 4:00 na yamma.
"Amma tawagarmu ta ci gaba da karfafa mata gwiwa, da bata dalilai na yin farin ciki da fatan kammala biki cikin nasara."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da amarya ta karaya saboda rashin zuwa masu abinci

Bidiyon mai tsuma zuciya ya ja hankali sosai, yana mai nuna muhimmancin karfafawa juna gwiwa a lokacin da ake fuskantar kalubale.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi, Ta Bayyana Dalilanta

Wasu mutane a sashin sharhi sun bayyana cewa wasu ne ke kokarin kawo tangarda a ranarta ta farin ciki.

@Sharkii ya yi martani:

"KI AMBACI SUNA DA KUNYATA MASU ABINCIN."

@somethingsomething ta yi martani:

"Abubuawa da dama sun tafi ba daidai ba. Imma dai an yi mata zagon kasa ko alamu ne na cewar kada ta yi shi."

@debstam ta yi martani:

"Don Allah fadi sunayen masu abincin don kada mu yi kuskuren zabarsu."

Dan Najeriya da ke turai ya cika da mamakin ganin motocin da ake tasi da su

A wani labarin, wani dan Najeriya da ke zaune a turai ya cika da mamaki lokacin da ya ga wasu tsadaddun motocin alfarma baje a titi a matsayin tasi.

A wani bidiyo da ya yada, mutumin mai suna Emeka Prosper, ya nunawa mabiyansa manyan motoci kamar su Mercedes Benz da Tesla da aka paka a kan hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel