Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda

Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce shugaban yan bindiga Ado Aleru da aka nada sarauta a Zamfara ya kashe fiye da mutum 100 a Katsina
  • Gambo Isah, Kakakin yan sandan Katsina ya sanar da haka yayin da ya ke martani kan sarautar da masarautar Yandoton Daji ta nada kasurgumin dan bindigan
  • Gwamna Aminu Bello Masari shima ya ce jihar Katsina ba ta yafe wa Aleru laifukan da ya aikata ba kuma har yanzu ana nemansa ruwa a jallo

Katsina - Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa shugaban yan bindiga, Ado Aleru, wanda aka nada sarauta ranar Alhamis da ta gabata a masarautar Yandoto Daji a Zamfara, har yanzu suna nemansa ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Rundunar yan sandan ta ce ana zargin Alero da kashe mutane 100 mazauna Jihar Katsina, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Yan Sandan Najeriya.
Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, Rundunar Yan Sanda. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin rundunar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke martani kan nadin sarautar da aka yi wa shugaban yan bindigan a Zamfara.

Isah ya ce rundunar ta ayyana neman Aleru ruwa a jallo don laifuka da suka hada da kisa, ta'addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a Jihar Katsina.

Ya kara da cewa kuma ana neman Aleru ruwa a jallo saboda kashe fiye da mutane 100 a kauyen Kadisau a karamar hukumar Faskari na jihar.

A watan Yunin bara ne rundunar ta ayyana neman dan bindigan mai shekaru 47 dan asalin karamar hukumar Tsafe na Zamfara ruwa a jallo, ta saka la'adar N5m a kansa - a rayye ko mace.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga Bayan Musayar Wuta, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura

Ana zarginsa da jagorancin tawagar yan bindiga da ke addabar mutanen jihohin Katsina da Zamfara.

Kwanaki kadan bayan an ayyana nemansa ruwa a jallo, Alero, kamar yadda aka rahoto ya jagoranci kai hari a kauyen Kadisau a ranar 9 a watan Yuni inda aka kashe mutane da dama wanda ba su ji ba ba su gani ba.

A bangarensa, Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya ce jiharsa ba ta yafe wa Alero ba.

Zamfara: Matawalle Ya Dakatar Da Sarkin Da Ya Nada Gogarmar Dan Bindiga Sarautar Sarkin Fulani

Tun farko, Gwamna Jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin Ƴandoto, Aliyu Marafa saboda naɗa shugaban yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, Sarkin Fulani, rahoton Daily Trust.

Matakin da masarautar ta dauka na nada ɗan bindigan sarauta ya janyo cece-kuce inda da dama suka soki naɗin sarautar da aka yi wa ɓata garin.

Kara karanta wannan

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

Amma, cikin wata sanarwa da sakataren gwamnati, Kabiru Balarabe ya fitar, gwamnatin ta nesanta kanta daga matakin sarkin, ta kuma dakatar da sarkin sannan ta kafa kwamiti don bincike kan lamarin, Daily Nigerian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel