'Yan Sanda Sun Kashe Kasurgumin Dan Bindiga a Arewa, Sun Kwato Muggan Makamai

'Yan Sanda Sun Kashe Kasurgumin Dan Bindiga a Arewa, Sun Kwato Muggan Makamai

  • ‘Yan sanda a jihar Sokoto sun hallaka wani kasurgumin dan ta’addan da ya addabi mazauna jihar
  • An bayyana yadda aka yi dauki ba dadi dashi kafin daga bisani a hallaka shi a wani dajin jihar da ke Arewa
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da barnar ‘yan bindigan da ke dauke muggan makamai

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Sokoto - Kwanaki kadan bayan kama wasu mutane 15 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta sake kashe wani dan bindiga tare da kwato bindiga kirar AK47 a hannunsa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i ya fitar a ranar Lahadi a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Kaigama.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su sha kyautar miliyoyi daga Wike, sun kamo dan bindigan da ya addabi jama'a a Abuja

'Yan sanda sun hallaka shugaban 'yan bindiga
'Yan sanda sun sheke wani kasurgumin dan bindiga a Sokoto | Hoto: NPF
Asali: Facebook

An kwato bindigogi a hannun tsagerun ‘yan bindiga

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an kama mutane biyar da AK47 guda uku da harsashi 90 a hanyarsu ta zuwa Tambuwal a wani yunkuri na zuwa yin garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce, bincike ya nuna cewa kasurgumin mai suna Bello Hantsi da aka fi sani da Mai Dubu-Dubu, ya kasance shugaban ‘yan bindiga kuma mai samar da makamai da alburusai ga barayin, The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan, yayin da ya yaba wa kwazon jami’ai, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da baiwa rundunar da sauran hukumomin tsaro a jihar damar samun bayanai aikata laifuka a kan lokaci.

A ci gaba da ba ‘yan sanda bayanan sirri, inji kwamishina

Ya ce irin wadannan bayanai za su bai wa rundunar da sauran jami’an tsaro damar daukar kwararan matakai a kan duk wani dan ta’adda a jihar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kona mutane 12 har lahira, sun kuma babbake gidaje 17 a wata jihar Arewa

Ya kuma nanata kudurin rundunar na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar a karkashin jagorancinsa.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin Arewa masu Yamma da ke yawan fama da barnar tsagerun ‘yan ta’addan da ke kisa da sace mutane.

An kamo kasurgumin dan bindigan da ya addabi Abuja

A wani rahoton, kun ji yadda 'yan sanda suka yi nasarar kame wani kasurgumin dan bindigan da ake zargin na daga cikin wadanda suka addabi Abuja.

A tun farko, ministan Abuja ya ba da sanarwar zai ba da kyautar kudi N20m ga duk wanda ya kamo 'yan ta'adda.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kafin daukar matakin da dokar kasa ta tanada kan wadanda aka kamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel