An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis

An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis

- Hukumar NDLEA ta yi nasarar kame wata tsohuwa dake sayar da muggan kwayoyi tare da jikarta

- Hakazalika ta kame wasu mata biyu su ma dake harkar sayar muggan kwayoyi a wani otal

- Shugaban NDLEA ya bada umarnin ci gaba da aikin kame dukkan masu hada-hadar muggan kwayoyi

Jami'an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wata tsohuwa 'yar shekara 80 da jikarta 'yar shekaru 19 ciki har da wasu mata biyu, da laifin sayar da muggan kwayoyi kamar hodar iblis, methamphetamine, tramadol, swinol, da skuchies.

Wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa an cafke wadanda ake zargin ne bayan samamen sirri da kuma bin diddigin wuraren da suke.

Ya kara da cewa sama da kiligiram 192 na hodar iblis da sauran abubuwan da suka shafi kwaya daga wadanda ake zargin an kwato su ne yayin da aka kame tsohuwar, jikarta, da wasu mata biyu; Tessy Matthew da Blessing Adesida, Channels Tv ta ruwaito.

KU KARANTA: Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja

An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Dake Ta'asar Sayar Da Hodar Iblis
An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Dake Ta'asar Sayar Da Hodar Iblis Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Tsohuwar, Mary Adebayo, da jikarta, Funmilola Adebayo, an kame su ne da misalin karfe 6:30 na safiyar Lahadi a layin Ayeyemi, da ke karamar hukumar Akure ta kudu.

A yayin samame, an sami nasarar gano: Skuchies - kilogiram 149, hodar iblis - ganyen maye giram 11, methamphetamine - giram 17 da - giram 3.

An kuma gano tabar wiwi - kilogiram 4.914, swinol - giram 8 da tramadol - giram 49. Haka kuma daga ciki an kwato firji mai zurfi guda biyu da babur kirar TVS.

A wannan ranar, da misalin karfe 1:30 na rana, wani samamen da aka kai a Otal din Rate, da ke kan titin Care, a karamar hukumar Akure ta Kudu ya kai ga kame Tessy Mathew mai shekaru 25 wanda aka kwato kilogiram 33 na skuchies a hannunta.

Bayan bincikenta na farko, nan take aka ci gaba da bin diddigin lamarin, wanda ya kai ga cafke Blessing Adesida mai shekaru 25 a yankin Oshinle na karamar hukumar Akure ta Kudu.

Muggan abubuwan da aka gano daga hannunta sun hada da skuchies - kilogioram 3 da tabar wiwi - giram 7 kuma ana ci gaba da bincikar sauran mambobin aikata laifin.

A sakamakon haka, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya) ya umarci mukaddashin Kwamandan rundunar ta Ondo, Callys Alumona da ta fara farautar sauran mambobin kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi cikin gaggawa.

KU KARANTA: Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

A wani labarin, Gwamnatin tarayya za ta gurfanar da wadanda ake zargi su 400 da aka cafke da laifin tallafawa ‘yan kungiyar Boko Haram da 'yan bindiga, Jaridar The Cable ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin ne a wani samamen hadin gwiwa daga hukumomin leken asirin tsaro (DIA), da sashin tsaro na farin kaya (DSS), da sashin tattara bayanan kudi na Najeriya (NFIU) da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN).

An kama su a Kano, Borno, Abuja, Lagos, Sokoto, Adamawa, Kaduna da Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.