Gwamnan Arewa Ya Zargi Wasu da Hadin Baki Da ’Yan Nijar Don Kifar da Shi a Mulki, Ya Fadi Dalili

Gwamnan Arewa Ya Zargi Wasu da Hadin Baki Da ’Yan Nijar Don Kifar da Shi a Mulki, Ya Fadi Dalili

  • Yayin da rashin tsaro ke kara kamari a jihar Benue, gwamnan jihar ya zargi wasu 'yan jihar da kokarin kawo tsaiko
  • Gwamna Alia Hyacinth ya zargi wasu 'yan jihar da hadin baki wurin gayyatar makiyaya daga Nijar don kifar da gwamnatinsa
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 18 ga watan Faburairu a cocin gidan gwamnati da ke birnin Makurdi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya zargi wasu 'yan jihar da hadin baki don kifar da gwamnatinsa.

Alia ya ce akwai wasu da suka hada baki musamman da 'yan kasar Nijar don kawo cikas a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan PDP ya tausayawa ma'aikata, ya tsawaita biyan kudin rage radadi har wata 6

Gwamnan APC ya zargi wasu 'yan kasar ketare da neman kifar da shi
Gwamna Alia na Benue ya bukaci hadin kan jami'an tsaro a jihar. Hoto: Alia Hyacinth.
Asali: Facebook

Mene gwamnan ke zargi a Benue?

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 18 ga watan Faburairu a cocin gidan gwamnati da ke Makurdi a jihar Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don dakile ayyukan wadannan bata gari a jiharsa, cewar The Nation.

Ya ce rahoton da suka samu shi ne ana gayyatar wasu makiyaya daga Nijar da nufin shigowa Benue don kawo matsala a mulkinsa.

A cewarsa:

"Ina jin bakin cikin abin da wasu 'yan Benue ke yi, abin da suke yi shiryawa ba alkairi ba ne ga jama'ar wannan jiha.
"Rahoton jami'an tsaro ya tabbatar da cewa wasu 'yan jihar na gayyatar makiyaya daga Nijar don kifar da gwamnatina, ba za mu yarda da hakan ba.
"Jami'an tsaro na iya kokarinsu don cafke masu hannu da kuma hukunta su, wannan ba ita ce jihar Benue da muke addu'ar samu ba, zabe ya wuce yanzu lokacin mulki ne."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin cafke masu boye kayan abinci

Sakon da gwamnan ya tura

Gwamnan ya ce jami'an tsaro sun shirya tsaf don ganin sun kare jama'ar jihar da kuma dukiyoyinsu gaba daya, cewar New Telegraph.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Donald Kumun, gwamnan ya bukaci makiyayan da su koma inda suka fito.

Gwamna Alia ya ce kuma duk 'yan jihar da ba za su zo a hada hannu wurin kawo ci gaba da su bar jihar tun da wuri.

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Benue

Kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai mummunan hari a kauyen Adijah a jihar Benue.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar ana fargabar 'yan bindigan sun hallaka bayin Allah da dama a harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel