Mahara Sun Kai Mummunan Hari a Arewa, Sun Salwantar da Rayuka Masu Yawa

Mahara Sun Kai Mummunan Hari a Arewa, Sun Salwantar da Rayuka Masu Yawa

  • Wasu mahara ɗauke da makamai sun kai sabon hari a ƙauyen Umogidi na ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue
  • Maharan dai a yayin harin da suka kai a ƙauyen sun halaka mutum biyu tare da jikkata wasu mutanen daban
  • Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo ya tabbatar da aukuwar harin inda ya ce ya zuwa yanzu hankula sun fara kwanciya a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu mahara ɗauke da makamai sun sake kashe mutum biyu a ƙauyen Umogidi, yankin Entekpa a gundumar Adoka, a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

Mazauna ƙauyen sun ce sabon kashe-kashen ya faru ne kwanaki biyu bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutum 17 a wasu ƙauyuka uku da suka haɗa da Iwili, Umogidi da Opaha a yankin Entekpa, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

Mahara sun kai hari a Benue
Mahara sun halaka mutum biyu a jihar Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wani ɗan yankin mai suna Adakole Joseph ya bayyana cewa mutanen biyu da aka kashe kawunsa ne ta ɗan uwansa yayin da wasu mutane marasa yawa suka jikkata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun sake kai hari Umogidi da yammacin ranar Alhamis, 8 ga Fabrairu, 2024, inda suka kashe wasu mutane, yayin da wasu kuma suka jikkata.

"Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum biyu. Ɗaya kawuna ne, dayan kuma ƙani ne."

Me hukumomi suka ce kan harin?

Alfred Oketa Omakwu, shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, shi ma ya tabbatar da faruwar harin ta wayar tarho, inda ya ce maharan sun kashe wasu matasa biyu, sannan sun yi artabu da sojoji.

Omakwu, ya ce hankali ya kwanta duk da barazanar da maharan suka yi da shan alwashin sake dawowa.

A kalamansa:

"Tun daga ranar Juma'a aka samu kwanciyar hankali kuma dakarun soji sun ƙaru. Amma har yanzu muna samun barazana daga gare su (maharan). An kashe matasanmu biyu a ranar Alhamis."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan halaka mutum 17 a wani sabon hari a jihar Arewa

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene kan harin, sai dai ta bayyana cewa har yanzi ba ta samu wani bayani ba dangane da harin.

Anene ta ce a taƙaice:

"Ban samu wani bayani ba dangane da harin."

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai, sun yi awon gaba da mutum 16 da suka haɗa da maza da mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel