Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi

Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi

- Babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana hanyoyin shawo kan matsalar tsaro da rashin aikin yi a kasar nan

- Yace inganta masana'antu tare da kara kaimi a harkar noma zai zama babbar hanyar samarwa matasa aikin yi a kasar nan

- Tsohon gwamnan jihar Legas din ya sanar da hakan a wani taro da ya shugabanta a Arewa House dake Kaduna

Jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana yadda za a iya shawo kan matsalar rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma sauran matsalolin da suka addabi mulkin kasar nan.

A yayin jawabi a taron shekarar 2021 na Arewa House, wanda ya shugabanta a ranar Asabar a Kaduna, Tinubu yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta saka hannayen jari masu yawa domin samar da ayyukan yi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, ya ce ya zama dole gwamnati tayi tunani mai zurfi wurin shawo kan kalubalen rashin aikin yi.

KU KARANTA: Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa

Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi
Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi. Hoto daga @Premiuntimes
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki

Kamar yadda yace, fushi tare da borin da matasa ke yi ne ya janyo tsananin talauci da lalacewar al'amura.

"Gina manyan bangarori kamar su wuraren ban ruwa, zai matukar taimakawa a fannin noma, shawo kan karatowar hamada kuma ya samar da ayyukan yi."

Tinubu ya kara da cewa ya zama dole gwamnati ta tabbatar da sabbin dokokin kasa a fannin masana'antu domin hakan zai sa masana'antun su zaburo da aiki tare da daukar matasa aiki.

A wani labari na daban, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da 'yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jihar Yobe inda 'yan Boko Haram ke horar da makiyayan dabarun yaki.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace 'yan ta'addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.

An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel