Manyan Kamfanoni 3 a Najeriya Sun Tafka Asarar Naira Biliyan 140, an Gano Dalili

Manyan Kamfanoni 3 a Najeriya Sun Tafka Asarar Naira Biliyan 140, an Gano Dalili

  • A yayin da kamfanoni suka tafka asarar biliyoyin naira a 2023 sakamakon karyewar darajar Naira, ana hasashen asarar 2024 sai ta fi yawa
  • Kamfanoni irin su BUA, Flourmills, Cadbury da ma bankuna irin su Unity na fuskantar barazana daga hauhawar farashin dalar amurka akan Naira
  • Ko a shekarar 2023, sai da kamfanoni uku suka tafka asarar sama da naira biliyan 140, wanda kuma ake ganin ba su ga komai ba sai a bana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu kamfanoni guda uku karkashin rukunin 'kamfanonin da ke sarrafa kayan da aka fi amfani da su (FMCG) sun tafka asarar sama da naira biliyan 140.

Kamfanonin da suka hada da kamfanin abinci na BUA, Flourmills da Cadbury Plc sun yi asarar ne sakamakon karyewar darajar Naira a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Jerin kasashe takwas da suka haramta yin bikin ranar masoya

Kamfanoni 3 sun tafka asarar biliyan 140 a Najeriya
Masana sun yi gargadin cewa kamfanoni na fuskantar tafka asara a 2024 fiye da wadda suka yi a 2023. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Cadbury Plc ya tafka asarar naira biliyan 36.93 yayin da BUA ya yi asarar naira biliyan 73.56, sai kuma Flourmills ya rasa naira biliyan 31.48.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Cadbury ya sake yin wata asarar naira biliyan 27.63, wanda ya rage kaso 2,228 daga ribar naira biliyan 1.3 da kamfanin ya samu a 2022, The Guardian ta ruwaito.

Abin da masana ke cewa game da tattalin arzikin Najeriya

Masana dai sun nuna damuwarsu kan yadda tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa wanda ke zama barazana ga kamfanonin sarrafa kayan masarufi.

Sun yi gargadi kan cewa idan har ba a shawo kan matsalar tattalin arzikin ba, to hakan na iya zama silar karyewar kamfanoni da dama a kasar.

A hannu daya kuma, shugaban kungiyar masu saka hannu jari ta Najeriya (ISAN), Mista Moses Igbeude, ya nemi kamfano da su rinka amfani da kayayyakin cikin gida don kaucewa yin asara.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya tona asirin wadanda ke da hannu a faduwar darajar Naira

Yadda tabarbarewar tattalin arziki zai shafi kamfanoni

Jagoran kamfanin Planet Capital, Paul Uzum ya ce yanzu da aka karya darajar Naira zuwa 1,430 akan dala 1, asarar da kamfanoni za su tafka a 2024 sai ta nunka wacce suka yi a 2023.

Yace wannan karyewar kudin kasar zai shafi kamfanoni da suka hada da Flourmills, Dangsuger, Cadbury, Guinness da ma wasu bankuna kamar Unity da sauransu.

Mataimakin kamfanin Highcap Securities, David Adonri ya ce kamfanonin da suke shigo da kayayyakin su daga kasashen waje za su jijjiga a wannan shekarar saboda karyewar Naira.

Abdul Samad Rabiu ya tafka asarar dala biliyan 2.7

Tun da farko, Legit Hausa ta ruwaito cewa attajirin Najeriya, kuma shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya tafka asarar dala biliyan 2.7.

Hakan kuwa ya faru ne biyo bayan karya dajarar Naira da gwamnati ta yi karo na biyu a cikin watanni takwas don daidaita tattalin arziki

Hakazalika wannan asarar ta ja attajirin ya koma na 448 a jerin masu kudin duniya bayan da shi ma Dangote ya tafka asarar biliyoyin dala

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel