Gombe: Tashin Hankali Yayin da Mummunar Gobara Ta Ɓarke a Barikin ’Yan Sanda, Bayanai Sun Fito

Gombe: Tashin Hankali Yayin da Mummunar Gobara Ta Ɓarke a Barikin ’Yan Sanda, Bayanai Sun Fito

  • Wata mummunar gobara ta babbake barikin 'yan sandan tafi-da-gidanka da ke a jihar Gombe a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu
  • Hukumar kashe gobara ta tarayya, reshen jihar ne ta bayyana hakan, inda ta ce an yi asarar kadarorin miliyoyin naira
  • Hakazalika hukumar ta ce ta yi nasarar kubutar da wasu kadadori daga barikin 'yan sanda ta kudin su ya kai naira miliyan 25.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gombe - A ranar Laraba ne gobara ta tashi barikin ‘yan sandan tafi da gidanka da ke Gombe, da ke a '34 PMF Squadron' daura da garin Kwami a jihar Gombe.

Kwamandan hukumar kashe gobara ta tarayya reshen jihar Gombe Ayuba Jonah-Sule ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Dalibin shekarar ƙarshe a jami'ar AUA ya kashe abokiyar karatunsa akan iPhone

Mummunar gobara ta babbake ofishin 'yan sandan Gombe.
Mummunar gobara ta lakume kadarar miliyoyin naira a ofishin 'yan sandan Gombe. Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Yadda gobarar ta lalata kadarori na miliyoyin naira

Ayuba Jonah-Sule wanda shi ma mataimakin konturolan kashe gobara ne ya ce gobarar ta babbake gaba daya ginin da ya hada da dakunan ajiye makamai da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yunusa-Sule ya kiyasta asarar da aka tafka da ta kai naira miliyan 100 inda ya jaddada cewa mutanensa sun yi nasarar ceto kadarorin da darajar su ta kai naira 25,000,000.

Ya ce:

"An kashe gobarar ne ta hanyar amfani da wani matsakaicin injin kashe gobara tare da hadin guiwar hukumar kashe gobara ta jiha da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya."

Gwamnan jihar Gombe ya ba 'yan kasuwa tallafin N5m

Yunusa-Sule ya kara da cewa, jami'an hukumarsa na kammala kashe wata gobara a unguwar Low-Cost din tarayya da ke kwaryar jihar aka sanar da su gobar ofishin 'yan sandan.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a ofishin 'yan sandan Kano

Wannan gobara dai na zuwa ne mako guda bayan da gwamnan jihar, Muhammadu Yahaya ya amince da fitar da naira miliyan 5 don tallafawa wadanda gobara ta lakumewa shaguna a kasuwar Makera da ke babbar kasuwar Gombe.

Gobarar ta babbake shagunan a ranar 25 ga watan Disamba, 2023, wanda ya yi sanadiyyar lalata kayan aiki da kayayyaki na miliyoyin naira.

Mummunar gobara ta tashi a ofishin'yan sandan jihar Kano

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa gobara ta babbake wani bangare na ofishin'yan sandan Nasarawa, jihar Kano.

Gobarar ta tashi ne a ranar Litinin, kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Mista Usaini Gumel ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel