Yadda Malamin Jami’a Ya Nemi Auren Daliba a Cikin Aji a Ranar Masoya, Bidiyon Ya Yadu

Yadda Malamin Jami’a Ya Nemi Auren Daliba a Cikin Aji a Ranar Masoya, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani malami a jami'ar jihar Abia (ABSU) ya haifar da hayaniya a cikin aji yayin da ya nemi auren wata daliba cikin bazata
  • A cikin wani bidiyo mai tsuma zuciya, dalibai sun fasa ihu yayin da malamin ya durkusa a kan gwiwarsa don neman matashiyar da amsa tayinsa na neman aurenta
  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon yayin da wasu 'yan Najeriya suka caccaki lamarin, suna bayyana shi a matsayin wanda bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Anucha Wisdom, wani malami a jami'ar jihar Abia (ABSU), ya nemi auren wata daliba a cikin aji a ranar masoya.

Malamin ya tsuma zuciyar matashiyar yayin da ya durkusa a gabanta dauke da zobe a hannunsa inda sauran dalibai suk dungi karfafa mata gwiwa.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Malami ya nemi auren dalibarsa
Yadda Malamin Jami’ar Ya Nemi Auren Daliba a Cikin Aji a Ranar Masoya, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Within Nigeria
Asali: Facebook

Wani bidiyo da Within Nigeria ta wallafa ya nuno matashiyar tana kokarin mayar da hawayenta yayin da ta amsa tayin Wisdom.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan take ta amsa tayin nasa sannan ta mika hannunta don ya sanya mata zoben alkawarin. Lamarin ya jefa dalibai cikin farin ciki.

Wasu jama'a sun jinjinawa soyayyar malami da dalibar, yayin da wasu suka caccaki abun.

Jama'a sun yi martani yayin da malami ya nemi auren daliba

Chukwura Chekwubechukwu ta ce:

"Daya daga cikin malamaina a wancan lokacin ya auri abokiyar karatuna.... Shaaaa idan ya durkusa, ba a gabanmu ba.
"Kwatsam bayan kammala karatu muka ga katin gayyata."

Meek Stizz ta ce:

"Diyata ba za ta auri malamin jami'a ba.
"Ina taya su murna ina yi masu fatan alkhairi."

Roberto J Nok ya ce:

"Ya gama ya je ya amsa tuhuma akwai abubuwan da ya kamata mutum ya yi amfani da kansa wajen tunani kafin ya aikata shi. A matsayinsa na malamin jami'a a makaranta guda wannan ba daidai bane."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Mstr Smeev ya ce:

"Ban yarda da yarinyar nan ba. Me yasa bata bude baki ba, sannan ta sanya hannaye biyu kan kirji?"

Mata da gudu da kudin miji

A wani labari na daban, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel