Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

  • Mutane sun yi takansu yayin da wata mota ta kama da wuta ba zato ba tsammani a hedkwatar jam'iyyar APC mai mulki a birnin Abuja
  • Rahotanni daga ganau sun nuna cewa motar ta taho ne daga Otal din Barcelona, inda kwatsam ta kama da wuta amma tuni aka shawo kan lamarin
  • Wani Abudullahi ya ce lamarin ya zo da sauki da taimakon hanzarin direban motar amma ba don haka ba da yanzu wani labarin ake daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An shiga yanayin tashin hankali a sakateriyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa yayin da wata mota ta kama wuta a ƙofar shiga wurin a Abuja.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

Motar da aka yi mata fentin ja, mai lamba TSE-423-AA, jihar Benuwe, ta fito ne daga otal din Barcelona da ke kan titin Blantyre, a unguwar Wuse 2 Abuja, kwatsam ta kama wuta.

Shugaban APC na ƙasa, Ganduje.
Tashin Hankali Yayin da Wata Mota Ta Kama da Wuta a Kusa da Sakatariyar APC Ta Kasa Hoto: OfficialAPC
Asali: Twitter

Wakilin jaridar Daily Trust, wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya nemi jin ta bakin direban motar da ta kama ci da wuta amma mutumin ya ƙi yarda ya yi magana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin ana kokarin tsige Ganduje daga shugaban APC?

Lamarin ya faru ne a lokacin da wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC daga yankin Arewa ta Tsakiya suka gudanar da wani ralin goyon bayan Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Mambobin jam'iyyar APC da suka yi gangamin sun bayyana cewa ba su goyon bayan a tsige Ganduje daga kujerar shugaban APC na ƙasa kafin ƙarewar wa'adinsa.

Yadda aka taru aka kashe wutar motar

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya

Bayanai sun nuna wasu ma'aikatan sakateriyar da ke kusa da ƙofar shiga sun ɗaga murya suna faɗin "wuta, wuta" lamarin da ya sa jama'a suka fara gudun neman tsira.

Har sai da wasu direbobi da jami'an tsaro suka kai ɗauki wurin sannan aka yi nasarar kashe wutar.

Bayan kashe wuta, sai aka janye jar motar daga kofar shiga, aka yi fakin ɗinta a kusa da Kotun Stallion da ke kan titin Blantyre.

Wani ganau da ya bayyana sunansa da Abdullahi, ya ce, “Direban ya yi hanzari sosai, ba don haka ba wataƙila da ranar Laraban nan da zama baƙa."

PDP ta tabbatar da naɗin shugaban BoT

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta tabbatar da Sanata Adolphus Wabara a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BoT) na ƙasa.

A taron BoT karo na 76 da aka yi ranar Talata, an kuma naɗa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Maƙarfi, a matsayin sakataren kwamitin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel