Mijina Yana Min Sata Don Ya Siya Kwayoyi, Matar Aure Mai Neman Saki a Kotu

Mijina Yana Min Sata Don Ya Siya Kwayoyi, Matar Aure Mai Neman Saki a Kotu

  • Wata kotu mai zamanta a Centre-Igboro, jihar Kwara ta raba auren wasu ma'aurata bayan da matar ta shigar da karar mijinta a gaban kotun
  • Rahotanni sun bayyana cewa matar ce ta nemi a raba auren nasu saboda mijin nata yana shayeye kuma yana satar mata 'yan kudade
  • Sai dai mijin ya musanta satarwa matar kudi amma ya amsa cewa yana shan sigari, wanda mai shari'ar ya datse igiyar auren

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Wata matar aure mai suna Ramat Joke a ranar Talata ta roki wata kotu da ke Centre-Igboro, Ilorin, da ta datse igiyar aurenta a kan cewa mijinta, Habeeb Atanda ya koma mashayin kwaya.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Joke a cikin karar neman sakin ta shaida wa kotu cewa ba ta da masaniyar cewa Atanda na shaye-shayen kwayoyi kafin aurensu.

Matar aure ta nemi kotu ta tilasta mijinta ya sake ta saboda yana shaye-shaye.
Matar aure ta nemi kotu ta tilasta mijinta ya sake ta saboda yana shaye-shaye.
Asali: UGC

Ramat ta roki kotu ta raba aurenta da Habeeb

Joke ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sai bayan da muka yi aure ne na gano yana tu'ammali da miyagun kwayoyi da shan sigari. “Duk kokarin da na yi don ganin na canza shi ya ci tura.
“Mijina ya na min sata don ya yi amfani da kudin wajen sayen kwayoyi, kuma shi ba ya iya daukar nauyi na."

Da yake mayar da martani, Mista Atanda ya musanta cewa yana satar kudin matarsa amma ya yarda cewa ya na shan sigari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Atanda ya ce matarsa ​​ce ta jawo masa har ya rasa aikin sa saboda yawan takurar ta. A karshe kuma ya amince da bukatar matar na sakinta.

Kara karanta wannan

Arziki mai rana: Yadda matashi ya siya abincin mai talla gaba daya, ya rabawa marasa galihu

Kotu ta karbi rokon Ramat, ta warware auren

Alkalin kotun, AbdulQadir Umar, ya ce ana son aure ya zama na fahimtar juna, wanda ya kamata ya zama mai cike da taimakekeniyar juna.

“Amma idan aure yana cike da matsaloli, ana iya kawo maslaha ta hanyar yin sakin.”

- A cewar Umar.

Don haka Malam Umar ya raba auren, ya kuma umurci matar da ta yi idda na wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kafin ta kara yin wani auren.

Matar aure ta roki kotu ta raba aurenta na shekaru 20

A baya bayan nan ne Legit Hausa ta ruwaito cewa wata matar aure ta mai suna Tawakalitu Olayiwola ta roki wata kotun kostomare da ta datse igiyar aurenta na shekaru 20.

Mis Olayiwola wacce 'yar kasuwa ce dake zama a birnin Ibadan, jihar Oyo ta shaida wa kotun cewa tana fama da hawan jini sakamakon yawan masifar mijin nata.

Ta kuma bayyana cewa mijin nata na zargin tana bin wasu maza a waje, sannan yana da saurin fushi wanda ke sa shi dukanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel