Idan ta gama idda zan aure ta inji mai neman Matar da ta rasa auren ta saboda Buhari

Idan ta gama idda zan aure ta inji mai neman Matar da ta rasa auren ta saboda Buhari

Kwanan nan ne mu ka ji labarin yadda wani Magidancin ya rabu da Mai dakin sa, a dalilin kurum kaunar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ta ke yi. Tuni labarin na su dai ya zagaya Duniya.

Soyayyar shugaba Muhammadu Buhari ne ya jawo wannan mata ta rasa auren ta, sai dai kuma, haka-zalika soyayyar da wasu ke yi wa shugaban kasar ya sa wasu kuma su na neman wannan Baiwar Allah da aure yanzu haka.

Wani Bawan Allah ya bayyana cewa a shirye yake ya auri wannan Mata da Mijin ta ya sake ta babu wani dalili illa kurum tana goyon bayan shugaba Buhari. Zakariyya Abdullahi yace shi zai so ya auri wannnan Baiwar Allah.

KU KARANTA: Yadda Amaechi ya jefa ni cikin babbar matsala ana zaune kalau - Buhari

Malam Zakariyya Abdullahi yake cewa duk da bai taba ganin wannan Mata ba, amma zai so ya aure ta da zarar ta kammala iddar ta. Malam Zakariyya ya bada lambar wayar sa domin a tuntube sa a lokacin da ya fara jin labarin ta.

Bisa dukkan alamu dai wannan Bawan Allah yana kaunar shugaba Buhari kamar wannan mata don haka yake neman ta zama Mai dakin sa. Soyayyar shugaban kasar ce dai tayi sanadiyyar mutuwar wannan aure a Garin Filato.

Dazu kun ji cewa ana ta surutu an rasa inda Uwargidar Shugaban kasa Buhari ta shige a Najeriya daf da zaben 2019 inda mijin ta ke neman tazarce. Tuni aka fara rade-radin Hajiya Aisha Buhari ba ta da lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: