Kura kurai 5 da maza ke yi wajen neman aure
Mazaje da dama sukan yi kuskure wajen neman matan aure inda shi aure kuma wani ginshiki ne na zamantakewa da Allah (SWT) ya tsara tsakanin mace da namiji, Shi ne kadai tsarin rayuwar da Manzo (SAW) ya amince mu yi a tsawon rayuwarmu. Hadisai da bayyanan malamai da dama sun gudana kan falala, kima da darajar aure, shi yasa ake son mutum yayi kafa kafa wajen zaben mata ko mijin aure.
Legit.ng ta tattaro daga majiyar mu wadansu kurakurai bakwai da maza keyi wajen neman matan aure:
1. Yin karya: Karya tana daga cikin irin abubuwan da ke zubar da mutuncin mutum wajen wacce zai aura. Ka ga matashi yana yi wa yarinya karya, ai shi mai arziki ne, idan ta aure shi ta huta. Ya rika karbar aron abubuwan duniya don ya rude ta. Wannan shi ne mataki na karshe a rashin Wayewa, da fatar masu irin wannan halin za su fadaka su daina.
2. Rowa: Dukkan mace tana son kyauta, ya zamana hannun saurayi a bude yake. Duk da ba a dora sharadin aure kan yin kyautar kudi ba, amma Monzon Allah (saw) ya fadi cewa, “Zuciya tana jawuwa bisa son wanda yake kyautata mata, sannan tana kin wanda ya munana mata”. Kenan ashe kyauta za ta iya taka muhimmiyar rawa a wajen neman aure.
3. Rashin Wayewa: Sau tari wasu mazan sukan gabaci Mace, su rika nuna tsanin wayewarsu ta zamani. A ganinsu wannan ne dalilin da zai sa su karbu wajen Mace. Sannan a hakan kuma saboda rashin wayewar tasu, babu abin da za su fi mayar da hankali a kai illah neman wacce wai take da wayewar Zamani.
KU KARANTA: Farashin wutar lantarki zai yi sama
4. Jahilci: Jahilci na daga cikin abun da ke sawa ka samu matsala da wadda kake nema, musamman ma idan ta gano kai jahili ne,to ai ka gama yawo! Don Mace na son namiji mai ilmi duka biyu, wannan zai sa ta soka.
Kazanta:Tana daga cikin abubuwan dake sa ka rasa kima a wajen Mace saboda gaskiya mata na da tsabta yadda ya kamata, saboda haka ba sa son namiji kazami. Abin alfaharin Mace ne ta nuna ka a gaban kawayenta ka yi wanka mai kyau, ka hadu!
5. Shishigi: yana dai daga cikin kuskuren da maza ke tafkawa wajen matar da zae aura. Ka ga namiji ya fiye tambayoyi a cikin a halin gidansu, mahaifiyarta mahaifinta, ko ya dinga yi mata tambayoyin da ba su zama dole ba. Lallai wannan na saka ka rasa kimarka wajen macen da za ka aura.
Wadannan kurakuren na taka muhimmiyar rawa wajen zaben aboki ko abokiyar zama. Da fatan za mu amfana.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng